Kotu ta tsare matar aure kan zargin kashe jaririn mijinta
Ana zargin matar da kashe ɗan mijinta mai kwanaki uku da haihuwa ta hanyar guba.
Kotun Majistire mai lamba 2 da ke Kano ta bayar da umarnin a tsare wata matar aure mai suna Zayya Magaji bisa zargin kashe ɗan mijinta.
A cewar masu gabatar da ƙara, Zayya ta haddasa mutuwar ɗan mijinta mai kwanaki uku da haihuwa ta hanyar guba. Sai dai ta musanta aikata laifin.
Wacce ake tuhuma, mazauniyar kauyen Danbamgo da ke Karamar Hukumar Kabo a Jihar Kano, an gurfanar da ita a gaban kotu ta hannun Lauyan Gwamnati, Barrista Muhammad Aliyu.
Lauyan gwamnati ya shaida wa kotu cewa an riga an mika fayil ɗin shari’ar zuwa Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano domin samun shawarar doka.
- Kotu ta daure masu taimakon Boko Haram shekara 10 zuwa 40 a kurkuku
- Sheikh Abduljabbar ya nemi kotu ta dawo da shi Kano daga Gidan Yarin Kuje
Mai shari’a Auwal Yusuf, wanda ya jagoranci zaman, ya amince da buƙatar dage shari’ar tare da bayar da umarnin a tsare wacce ake tuhuma a gidan yari.
An dage shari’ar zuwa ranar 29 ga Afrilu domin ci gaba da sauraron ƙarar.