Kotu ta tsare matar da ake zargi da kashe mijinta a Kano

Kotu ta ba da umarnin tsare matar a Gidan Kaso har zuwa lokacin da za ci gaba da shari’ar.

Kotu ta tsare matar da ake zargi da kashe mijinta a Kano

Kotu

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Filin Hockey a Jihar Kano, ta ba da umarnin tsare wata matar aure a Gidan Kaso kan zargin kashe mijinta.

An dai soma sauraron karar kisan mutumin mai suna Sabiu Ado na unguwar Maidile da ke karamar Hukumar Kumbutso ta jihar, wanda ake zargi mai dakinsa ce silar ajalinsa.

Aminiya ta ruwaito cewa, kotun dai tana tuhumar matarsa, Firdausi Isa da kashe mijinta yayin shari’ar da aka soma a ranar wannan Jumaar.

Bayanai sun ce lamarin ya faru ne tun a bara, bayan da wata sa’insa ta shiga tsakanin ma’auratan ya sanya ake zargin matar ta daba wa mijin nata wuka kuma a sanadiyar haka rai ya yi masa halinsa.

Lauyan da ke kara, Barista Lamido Sorondinki ya gabatar wa kotun wani mutum mai suna Muhammad Yusuf  a matsayin shaida wanda makwabci ne ga marigayin.

Lauyan da ke kare matar da ake tuhuma, Abdul Waziri, ya kalubalanci shaidar da aka gabatar wa kotun da cewa bai aminta da gaskiyarsa ba.

Dangane da hakan ne lauyan mai gabatar da kara ya nemi kotun ta sanya musu wata rana domin ya kara gabatar mata da shaidar da lauyan wadda ake tuhuma zai aminta da ita.

Bisa wannan bukatar ce, alkalin kotun Abdullahi Halliru, ya ba da umarnin tsare matar da ake tuhuma a Gidan Dan Kande, yayin da ya dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Fabarairun 2024.