Kotu ta tsare matasa 8 kan kisan dan sanda

Wata kotun majistare da ke Ibadan, babban birnin Oyo, ta tsare wasu matasa takwas ranar Alhamis, bisa zargin su da laifin satar mutane da kisan kai. Dan sanda mai gabatar da kara Insfekta Femi Oluwadare ya bayyana wa kotun cewa matasan masu shekara 20 zuwa 34 sun aikata laifin farko ne ranar 28 ga watan […]

Kotu ta tsare matasa 8 kan kisan dan sanda

Daurin Kotu

Wata kotun majistare da ke Ibadan, babban birnin Oyo, ta tsare wasu matasa takwas ranar Alhamis, bisa zargin su da laifin satar mutane da kisan kai.

Dan sanda mai gabatar da kara Insfekta Femi Oluwadare ya bayyana wa kotun cewa matasan masu shekara 20 zuwa 34 sun aikata laifin farko ne ranar 28 ga watan Oktoba da karfe 5:00 na yamma, a unguwar Guru Maharaji da ke Ibadan.

“Bayan kama su an same su da bindiga kirar Ak-47, da wata matashiya da suka sace mai suna Oluwatomilola Ogundare.

“Daga nan ne suka bukaci  mahaifinta ya biya su kudin fansa N10m, kafin su sake ta,” in ji shi.

Oluwadare ya ce baya ga haka sun harbe wani dan sanda mai suna Rotimi Akerele har lahira, laifin da ya saba wa sashi na 316(3) da na 319, da na 516 na kundin manyan laifuka.

Alkalin kotun Mista E.A Idowu ya yi watsi da bukatar wadanda ake kara na bada beli, tare da bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali.

Daga nan ne ya dage zaman shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Fabrairu, 2023.