Kotu ta tsare matasan da suka boye budurwa a Dutse

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta Dutse a karkashin Mai shari’a Aliyu Muhammed Hadeja ta tura wasu matasa kurkuku don zaman jiran shari’a saboda zarginsu da boye wata budurwa (an sakaya sunanta) ’yar kabilar Tula daga Jihar GombeBudurwar mai kimanin shekara 20 ana zargin ta hada lambobin waya ne ta kira wani direba mai suna Husaini […]

Kotu ta tsare matasan da suka boye budurwa a Dutse
Kotu ta tsare matasan da suka boye budurwa a Dutse

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta Dutse a karkashin Mai shari’a Aliyu Muhammed Hadeja ta tura wasu matasa kurkuku don zaman jiran shari’a saboda zarginsu da boye wata budurwa (an sakaya sunanta) ’yar kabilar Tula daga Jihar Gombe
Budurwar mai kimanin shekara 20 ana zargin ta hada lambobin waya ne ta kira wani direba mai suna Husaini Sunusi da ke kauyen Alawa a karamar Hukumar Gaya ta Jihar Kano, suka zanta a kan zai ba ta mafaka bayan ta gudo daga garinsu, kuma ya kai ta gidan da yake haya a Unguwar Kachi a karamar Hukumar Dutse inda ake zargin shi da wasu abokansa suna kwana da ita.
An shaida wa kotun cewa matasan unguwar Kachi ne suka sanar da mai unguwar Alhaji Shafi’u Abdullahi halin da yarinyar take ciki, shi kuma ya sa aka kama matasan  da aka tambayi Husaini Direba a gaban mai unguwar sai ya ce bai kwanta da ita ba.
Sai dai wani kanen mahaifiyar yarinyar ya bukaci matashin ya biya shi Naira dubu 30 da ya kashe wajen cigiyar ’yarsu sakamakon boye ta da ya yi. Amma sai daya daga cikin abokan matashin da ya ji an ce za a biya wannan kudi kuma za a tafi da yarinyar a yi mata gwaji ko ta samu ciki sai ya ki amincewa, wannan ya sa mai unguwar ya kira jami’an tsaro suka kama su aka gabatar da su a gaban kotun.
Abokin mai suna Adamu Abubakar Gwadda ma’aikacin kamfanin Satrico da ke aikin hanya a jihar ya ce ba ya cikin wadanda ake zargi sun kwana da yarinyar, shawara ya bayar a gaban mai unguwa saboda haka aka hada da shi aka kama.
Da take fadar dalilinta na gudowa daga garinsu domin samun mafaka a wurin saurayin da ba ta taba gani ba, ta ce saboda za a yi mata auren dole da dan Hakimin Tula, kuma har gobe ba ta sonsa ba kuma za ta aure shi ba.