Kotu ta tsare matashi bisa zargin sata a majami’ar Abuja
Wani matashi dan shekara 20, Joseph Shagari da ke da zama a Unguwar Rogo, Karmo-Abuja, ya gurfana a gaban Kotun Lardi mai daraja ta daya da ke zama a garin Gwagwa-Abuja bisa zargin satar kayan majami’a.dan sanda mai gabatar da kara, Sani Idris na babban ofishin ’yan sanda na Karmo, ya shaida wa kotun a […]
Wani matashi dan shekara 20, Joseph Shagari da ke da zama a Unguwar Rogo, Karmo-Abuja, ya gurfana a gaban Kotun Lardi mai daraja ta daya da ke zama a garin Gwagwa-Abuja bisa zargin satar kayan majami’a.
dan sanda mai gabatar da kara, Sani Idris na babban ofishin ’yan sanda na Karmo, ya shaida wa kotun a yayin zamanta na Litinin da ta gabata cewa, daya daga cikin jagororin majami’ar ne ya kai karar al’amarin, inda ya sanar da cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar 11 ga Disamba, yana yunkurin cire kwanon rufi na majami’arsu mai suna Assembly God Church da ke garin na Karmo. Ya ce bayan an kama shi, an kuma fahimci bacewar wasu kayayyaki na majami’ar, inda ya ce shi ne ya sace su, sanan ya sayar da su ga mutane biyu. Ya ce kayayyakin, wadanda suka hada da kujerun roba 12 da na’urar amfilifaya 1 da lasifika 2 da kararrawar majami’a 1 da kuma bokiti 1, kimarsu ta kai Naira dubu 150. Ya ce ya sayar da su ne ga Tasi’u Dogara da kuma danyaro Muhammad, wadanda ’yan kasuwa ne da ke da zama a yankin Rake Junction, a nan Karmo.
An gurfanar da mutanen biyu tare da shi matashin, inda dan sandan ya ce gaba dayansu sun amince da aikata laifin a yayin bincike.
Da mai shari’a Muhammad Sulyman Ola ya waiwayi wadanda ake zargin, sun musanta aikata laifin, sannan suka bukaci a bada belinsu. Daga nan ne kuma ya bada umarnin a ci gaba da tsare su har zuwa lokacin da suka cika ka’idar beli, wanda ya hada da gabtar da amintaccen mutum da ke da zama a yankin da ke karkashin hurumin kotun ga kowannensu, wadanda kuma za su bada Naira dubu 100 ga kowane mutum guda, idan ya sulale.
An dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 27 ga watan Junairun badi.