Kotu ta tsare matashi bisa zargin yi wa ’yar firamare ciki

Wata kotun majistare da ke Suleja a Jihar Neja ta ba da umarnin tsare wani matashi mai suna Emmanuel Jatau, bisa zargin yi wa wata ’yar shekara 12 da ke aji uku a wata makarantar firamare a yankin ciki a lokacin hutun makaranta. karar wadda ta hadin gwiwa ce da hukumar makarantar da yarinyar ke […]

Kotu ta tsare matashi bisa zargin yi wa ’yar firamare ciki
Kotu ta tsare matashi bisa zargin yi wa ’yar firamare ciki

Wata kotun majistare da ke Suleja a Jihar Neja ta ba da umarnin tsare wani matashi mai suna Emmanuel Jatau, bisa zargin yi wa wata ’yar shekara 12 da ke aji uku a wata makarantar firamare a yankin ciki a lokacin hutun makaranta.
karar wadda ta hadin gwiwa ce da hukumar makarantar da yarinyar ke dalibta ta shigar tare da magabatanta a kotun ta hannun lauyarsu mai suna Florence Egbanu, ta bayyana cewa bayan sun gayyaci wanda ake zargin, ya amince ya yi lalata da yarinyar tare da sanar da su cewa zai aure ta, ba tare da nuna nadama a kan al’amarin ba.
Masu karar sun ce, al’amarin ya yi sanadin dakatar da karatunta da jefa iyayenta a cikin kunci, saboda haka, suna son kotun ta ladabtar da wanda ake zargin kan ci zarafin yarinyar da take hakkin yara.
Mai shari’a Mariya M. Isma’ila ta dage zaman sauraron karar zuwa ranar 20 ga Agustan nan, don yanke hukunci a kan ko wadanda suka shigar da karar na da hurumin shigar da ita a madadin yarinyar, sakamakon ja a kan hakan da lauyan wanda ake kara ya yi.
Kotun ta ba da umarnin a tsare wanda ake zargin zuwa lokacin.