Kotu ta tsare matashi kan sukan Gwamnan Sakkwato da matarsa

Kotu ta tsare matashi Shafi’u Umar Tureta kan zargin batanci ga Gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu da matarsa, Fatima.

Kotu ta tsare matashi kan sukan Gwamnan Sakkwato da matarsa

Kotu

Kotu ta bayar da umarnin tsare matashi Shafi’u Umar Tureta dan shekara 36 zuwa 6 ga watan Satumba 2024, don fara sauraren shari’ar zargin sa da batanci ga Gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu da matarsa, Fatima.

Alkalin Kotun Majistare ta daya Fati Hassan ta bayar da umarnin ne a hukuncin da ta yanke a ofishinta da ke harabar kotun a Sakkwato.

Lauyan matsahin, Barista Almustapha Yusuf Abubakar, ya shaida wa kotun cewa laifin wanda ake bayar da beli a kansa ne, don haka  suke son a ba su beli kafin ranar da kotu ta sanya.

Lauyan ya bayyana cewa bayan an karanto tuhumar, wanda ake zargi ya musanta aikata laifin.

Takardar ƙara da ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Insfekta Abdurrahman Mansur ya karanta ta ce, matashin ya “tura wani bidiyo a ranar 18/7/2023 na matar Gwamnan Sakkwato, Hajiya Fatima Ahmad Aliyu, tana bukin murnar ranar haihuwarta.

“Ka yi maganar karya kanta na cewa tana kari da almubazaranci a lokacin da talakawa ke cikin yunwa da damuwa.”

Tuhuma ta biyu ta ce, “sanya sakamakon jarabawar Gwamna Dakta Ahmad Aliyu na kammala sikandare da matakin F9 ka kira shi da baƙauye, wanda ba ya iya magana da Turanci, hakan ɓata suna ne, hakan ya sa ake tuhumar ka da aikata laifi.”

Sakataren yaɗa labarai na Jam’iyyar adawa ta PDP Jihar Sakkwato, Hassan Sahabi Sanyinnawal, ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta saki matashin domin bai aikata laifi ba.

A cewarsa, wannan abu ne dake nuna bi-ta-da-kullin siyasa wanda ba za su lamunci hakan ba.

Ya ce, “kan bidiyon matar gwamna ai masoyanta ne suka fitar da lamarin kowa ya gani suna buki ana yi mata karin kudi Naira da Fala, su ba su yi laifi ba, sai wanda ya yada?

“Kuma sanda aka yi bukin talaka baya cikin yunwa ne?”

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano