Kotu ta tsare matashin da ya kashe limami a Kano

Kotun ta dage sauraren shariar zuwa ranar 31 ga watan Janairu, 2024.

Kotu ta tsare matashin da ya kashe limami a Kano

Kotun Majistare da ke zamanta a unguwar Nomansland da ke Jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare matashin nan Yusuf Haruna da ake zargi da kashe wani limami mai suna Sani Shuaibu a gidan gyaran hali.

Ana dai zargin cewa Yusuf Haruna wanda mazaunin unguwar Tudun Nufawa ne ya caccaka wa marigayin wuka saboda tsawartar masa kan shan ganye a kusa da masallaci, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

Lauyar gwamnati wadda ita ce mai gabatar da kara, Barista Fatima Ado Ahmad, ta shaida wa kotun cewa ana tuhumar matashin da laifin kisan gilla, laifin da ta ce ya saba da sashe na 221 na kundin final kod.

Sai dai bayan karanta masa kunshin tuhumar da ake yi masa, wanda ake zargin ya musanta aikata laifin.

Har wa yau, an kuma gurfanar da mahaifin wanda ake tuhumar, Haruna Sale kan zargin boye dan nasa bayan ya aikata laifin kamar yadda mai gabatar da kara, Barista Fatima Ado Ahmad ta shaida wa kotun.

Sai dai shi ma mahaifin ya musanta aikata laifin, wanda ya ci karo da sashe na 167 na kundin final kod.

Lauyan wanda ake kara, Barista Ahmad Rufai da Barista Rabiu Sidi, sun nemi kotun ta bayar da belin sa, lamarin da mai gabatar da kara ta kalubalanta.

Mai shari’a Binta Ibrahim Galadanchi, ta bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali tare da dage sauraron shari’ar zuwa ranar 31 ga watan Janairu, 2024.