Kotu ta tsare matashin da ya kashe mahaifiyarsa a Ekiti

Ana zargin matashi da kashe mahaifiyarsa sannan ya yada gawarta a daji.

Kotu ta tsare matashin da ya kashe mahaifiyarsa a Ekiti

Kotu

Wata kotun majistare da ke zamanta a Ado-Ekiti ta ba da umarnin tsare wani matashi da ake zargi da kisan mahaifiyarsa bayan samun sabani da suka yi.

Alkalin kotun, Misis Titilayo Ola-Olorun ta hana a bayar da belin matashin mai shekara 35, inda ta ba da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali na Ado-Ekiti kafin a yanke masa da hukunci.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Mai shari’a Titilayo t kuma dage sauraron shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Fabrairun 2022.

Jami’in dan sanda mai shigar da kara, Bamikole Olasunkanmi, ya shaida wa kotun cewar wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 11 ga watan Janairu a unguwar Ipole-Iloro a Jihar Ekiti.

Olasunkanmi ya bayyana wa kotun cewa matashin ya kashe mahaifiyarsa Misis Olaitan Abiola mai shekara 75 a duniya.

Ya kara da cewa matashin ya yi amfani da sanda inda ya doke mahaifiyarsa a kai, wanda hakan ya yi sanadin shekawarta lahira.

Olasunkanmi ya ce nan take mahaifiyar matashin ta yanke jiki ta fadi cikin jini, kuma matashin ya dauki gawar ya jefar da ita a jeji.

Laifin da matashin ya aikata ya saba wa sashe na 319 na kundin manyan laifuka na Jihar Ekiti na shekarar 2012, a cewar Olasunkanmi.

A kan haka ne Olasunkanmi ya bukaci kotun ta hana matashin belin sannan ta ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar.

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50 a Kaduna

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54