Kotu ta tsare mutum hudu kan zargin fashi da fyade
Kotun Majistare ta Jihar Neja da ke Suleja, ta ba da umarnin tsare wasu mutum hudu da ake zargi da yin fashi a wani gida da tsakar dare tare da yi fyade ga wata matar aure da mijinta wanda jami’in kurkuku ne yake wajen aiki. Tun farko a yayin gabatar da karar a ranar Alhamis […]
Kotun Majistare ta Jihar Neja da ke Suleja, ta ba da umarnin tsare wasu mutum hudu da ake zargi da yin fashi a wani gida da tsakar dare tare da yi fyade ga wata matar aure da mijinta wanda jami’in kurkuku ne yake wajen aiki.
Tun farko a yayin gabatar da karar a ranar Alhamis din makon jiya, dan sanda mai shigar da kara Jonathan Garba ya shaida wa kotun cewa, matar ta sanar da ofishinsu na “A” Dibision da ke Suleja cewa, mutanen da ake zargi masu suna Peter Paul da Dabid Amos, da Emeka Peter da kuma Ibrahim Isma’ila, wadanda daya daga cikinsu abokin mijinta ne daya kuma shi ne ya yi aikin rufin gidansu, bayan sun kutsa cikin gidan inda take kwance da kanwarta da ’ya’yanta, sun yi mata fyade sannan suka dauki kayayyakin daki da suka hada da talabijin na bango da kwamfutar laptop da kayan kawa na mata da kuma tsabar kudi Naira miliyan daya da dubu 70.
dan sandan ya ce, abubuwan da ake zarginsu da aikatawa laifuffuka ne da suka saba wa sashi na 97 da 298 da kuma 283 na kundin dokoki na Final kod.
Da alkalin kotun Mai shari’a Mariya Isma’ila ta waiwaye su, wadanda ake karar sun musanta zargin, sannan suka bukaci a ba da belinsu, yayin da mai shigar da karar ya nemi a dage shari’ar don bai wa ’yan sanda damar neman shawara daga sashin shigar da kararraki na gwamnatin jihar.
Kotun ta yi watsi da bukatar wadanda ake zargin na a bada belinsu inda ta ba da umarnin a ci gaba da tsare su har zuwa ranar 17 ga Satumba, don ci gaban shari’ar.