Kotu ta tsare shi akan yunkurin yi wa ’yar shekar 10 fyade
Wata Kotun Majistare da ke Suleja ta Jihar Neja ta tasa keyar wani mai wanki da guda mai suna Nasiru Ilyasu gidan kurkuku, sakamakon yunkurin yi wa wata mai shekara 10 (an sakaya sunanta) fyade. Nasiru mai shekara 29 da ke wanki da guga a Unguwar Suleja Club, an gurfanar da shi ne a gaban […]

Wata Kotun Majistare da ke Suleja ta Jihar Neja ta tasa keyar wani mai wanki da guda mai suna Nasiru Ilyasu gidan kurkuku, sakamakon yunkurin yi wa wata mai shekara 10 (an sakaya sunanta) fyade. Nasiru mai shekara 29 da ke wanki da guga a Unguwar Suleja Club, an gurfanar da shi ne a gaban kotun bayan kama shi yana yunkurin yin lalata da yarinyar a ranar 31 ga Yulin da ya gabata a wani kango a unguwar, inda aka sanar da ofishin kungiyar ’yan sintiri wadanda suka kama shi.
Ofishin ya mika shi ga babban ofishin ’yan sanda na “B” Dibision da ke Suleja, wadanda suka gabatar da shi a gaban kotun a ranar Talatar da ta gabata.
dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Ibrahim Musa ya shaida wa kotun cewa mahaifin yarinyar ne, ya shigar da karar a wajensu, kuma a yayin bincike, wanda ake tuhumar ya amince da aikata laifin da ake zarginsa. Ya bayyana wa kotun cewa laifin ya saba wa sashi na 95 na Final Kod.
Bayan kotun ta karanto masa tuhumar da ake yi masa, alkalin kotun Mai shari’a Mariya Isma’ila, ta tambaye shi ko ya fahimci abin da ake zarginsa, inda wanda ake tuhumar ya ce ya fahimci zargin, kuma ya aikata laifin. Mai shigar da karar, ya bukaci kotun ta sassauta masa sakamakon rashin wahalar da kotun kamar yadda sashi na 157 na kundin manyan laifuffuka (CPC) ya bukata.
Mai shari’a Mariya ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 5 ga Satumba, don yanke hukunci tare da tura shi kurkuku zuwa ranar.