Kotu ta tura tsohon ministan lantarki zuwa gidan yari

Saleh Mamman ya kasance  ministan lantarki a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kotu ta tura tsohon ministan lantarki zuwa gidan yari

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsare tsohon ministan wutar lantarki, Injiniya Saleh Mamman, a gidan yari.

Kotun ta tsare tsohon ministan lantarkin a Gidan Yarin Kuje ne a ci gaba da shari’ar zargin sa da satar Naira biliyan 33.

Saleh Mamman ya kasance  ministan lantarki a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mai Shari’a James Omotosho ne ya ba da da umarnin a ranar Alhamis bayan Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) ta gurfanar da Inkiya Saleh Mamman kan tuhume-tuhume 12 kasu alaka da kudaden haram.

Dai sai tsohon ministan ya musanta aikata laifukan.

Daga bisani ne lauya EFCC, Olumide Fusika (SAN) ya bukaci kotun ta sa musu ranar gurfanarwa da ba da hujjoji a shari’ar.

Amma lauyan tsohon ministan, Femi Ate (SAN) ya shaida masa cewa ya gabatar da bukatar Bello kafin fara zaman kotun a ranar.

Duk da cewa alkalin ya tabbatar da samun takardar da misalin karfe 12:30 na rana, amma ya ce ba riga an shigar cikin kundin bayanan kotu ba.

A nasa bangaren, Ate ya roki kotun ta ba shi dama a ranar Juma’a domin yin suka kan rokon bangaren da ake kara.

Lauyan tsohon ministan bai ƙalubalanci bukatar ba.

Daga nan kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar Juma’a.