Kotu ta tsare wadanda aka kama da bindigogi a Taraba

Babbar Kotun Tarayya da ke Jalingo a Jihar Taraba ta bayar da umurnin a ci gaba da tsare wasu mutum shida da aka kama da manyan bindigogi da alburusai a lokacin rigimar addini na garin Ibbi.Alkalin Kotun Mai shari’a Stephen Pam ne ya bayar da umarnin lokacin da mai gabatar da kara ASP Ibrahim Buba […]

Kotu ta tsare wadanda aka kama da bindigogi a Taraba
Kotu ta tsare wadanda aka kama da bindigogi a Taraba

Babbar Kotun Tarayya da ke Jalingo a Jihar Taraba ta bayar da umurnin a ci gaba da tsare wasu mutum shida da aka kama da manyan bindigogi da alburusai a lokacin rigimar addini na garin Ibbi.
Alkalin Kotun Mai shari’a Stephen Pam ne ya bayar da umarnin lokacin da mai gabatar da kara ASP Ibrahim Buba ya shaida wa kotun cewa sojoji ne suka kama wadanda ake tuhumar da manyan bindigogin lokacin fadar na Ibbi.
Ya ce wadanda ake tuhumar sun hada da Awunike Jadiya da Enock Samaila da Solomon Samaila da Atoshen Adashen da Friday Irimiya da kuma Ashideku Ajadiya dukkansu mazauna garin Ibbi.
Mai gabatar da karar ya shaida wa kotun cewa an kama mutanen da bindigogi kirar AK47 guda uku da kananan bindigogi biyu da harsasai masu yawa.
ASP Ibrahim Buba ya ce hakan laifi ne da ya saba wa dokar mallakar makamai ta 516 ba tare izini ba.
Da Mai shari’a Stephen Pam ya tambayi wadanda ake tuhumar ko sun amince da aikata laifin da ake zarginsu, sai kowannensu ya musanta, inda mai gabatar da kara ya nemi kotun ta ba shi damar gabatar da shaidunnsa kuma alkalin ya amince.