Kotu ta tsare wadda ta sace dan kawarta don sayar da shi

Kotun Majistare da ke garin Jiwa a yankin Birnin Tarayya, Abuja ta bada umarnin tsare wata mace mai suna Obiager Okoerie, bayan ta amince da aikata laifin sace wani yaro mai shekara daya da wata takwas tare da shirin sayar da shi. dan sanda mai gabtar da kara Noah Moses na babban ofishin ’yan sanda […]

Kotu ta tsare wadda ta sace dan kawarta don sayar da shi
Kotu ta tsare wadda ta sace dan kawarta don sayar da shi

Kotun Majistare da ke garin Jiwa a yankin Birnin Tarayya, Abuja ta bada umarnin tsare wata mace mai suna Obiager Okoerie, bayan ta amince da aikata laifin sace wani yaro mai shekara daya da wata takwas tare da shirin sayar da shi. dan sanda mai gabtar da kara Noah Moses na babban ofishin ’yan sanda na garin Gwagwa, Abuja ya ce mahaifiyar yaron ne, ta sanar da su aukuwar lamarin a ofishinsu a ranar 1 ga watan Nuwamban nan. dan sandan ya shaida wa kotun cewa Obiager Okoerie, ta saci yaron ne a lokacin da ta je shagon mahaifiyarsa da ke kauyen Kaba inda ta dauke shi tana wasa da shi amma sai ta sulale da shi. Ya ce mahaifiyar yaron ta shiga damuwa sakamakon rashin dawowar wadda ake zargi, kuma ba ta gidan da take da zama a lokacin da a ka je. Ya ce daga nan ne mahaifiyar yaron tare da ’yan uwanta suka bazama zuwa tashoshin mota na Abuja inda a karshe suka gano ta a tashar Wazobiya da ke garin Gwagwalada tare da yaron a daidai lokacin da take kokarin shiga mota zuwa garin Aba da ke Jihar Abiya. Da alkalin kotun Mai sharia Josephine Obano ta waiwayi wadda ake zargin, ta amince da aikata laifin sannan ta ce wata malamar jinya ce da ke Aba ta Jihar Abiya ta ce ta kawo mata yaro mai kwatankwacin shekarun yaron, kuma ta ba ta Naira Dubu 100 a matsayin kafin alkalami. Mai shari’ar ta dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 18 ga Nuwamba don ba da damar ci gaba da bincike da gabatar da wadda ake zargi na biyu.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi