Kotu ta tsawaita wa’adin Giadom a matsayin shugaban APC
Babbar Kotun Birnin Tarayya ta tsawaita umurninta cewa Mataimakin Sakataren Jam’iyyar APC na Kasa, Victor Giadom, ya zama shugaban jam’iyyar na riko da kwana 14. Hukucin ya kara bude sabon babi a rikicin shugabancin jam’iyyar APC mai mulki, bayan Kwamitin Amintattunta na Kasa ya riga ya nada Mataimakin Shugabanta na Kasa na Yankin Kudu, Abiola […]
Babbar Kotun Birnin Tarayya ta tsawaita umurninta cewa Mataimakin Sakataren Jam’iyyar APC na Kasa, Victor Giadom, ya zama shugaban jam’iyyar na riko da kwana 14.
Hukucin ya kara bude sabon babi a rikicin shugabancin jam’iyyar APC mai mulki, bayan Kwamitin Amintattunta na Kasa ya riga ya nada Mataimakin Shugabanta na Kasa na Yankin Kudu, Abiola Ajimobi a matsayin shugaban riko.
Hakan ya biyo bayan tabbatar da dakatar da Shugaban Jam’iyyar na Kasa Adams Oshiomhole da Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta yi a ranar Laraba, ranar da kuma jam’iyyar ta nada Ajimobi ya yi riko.
Tun da farko, a ranar 16 ga watan Maris Mai Shari’a Samira Bature ta bayar da umurnin cewa Giadon ya ci gaba da jan ragamar jam’iyyar, bayan Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Mustapha Salihu ya bukaci haka a karar da ya shigar.
- Rudani: ‘Sabon shugaban’ APC ya soke tsarin jam’iyya kan zaben Edo
- Jam’iyyar APC ta nada Ajimobi ya zama shugabanta
Bayan dakatar da Osihomhole ne Mustapha Salihu ya sake neman a kara tsawaita wa’adin Victor Giadom, wanda tun a hukuncin kotun na farko, ta umurci a bar masa ragamar jam’iyyar, muddin ba Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar ne ya yanke hukunci sabanin hakan ba.
Rikicin APC ya kara kazancewa.
Rikicin shugabancin jam’iyyar APC ya dade yana tayar da kura, sai dai dawowarsa a baya-bayan nan ya fi saurin yin juyin waina.
Rikicin shugabancin jam’iyyar ya kara kazancewa bayan dakatar da Oshiomhole ta yadda aka ga manyan shugabanninta na kasa daga bangarori masu adawa da juna ke ikirarin shugabantar ta, a abin da ake ganin na da alaka da shirin zaben 2023.
Giadom na da goyon bayan kungiyar gwamnonin jam’iyyar da ma wasu tsoffin gwamnoni, yayin da Ajimobi ke da goyon bayan Kwamitin Gudanarwarta ta kasa da kuma madugun jam’iyyar Bola Ahmed Tinubu.