Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci kan zaben Gwamnan Kano
Kotun ta sanya ranar bayan shafe tsawon lokaci ana sauraren shari’ar.
Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Jihar Kano, ta sanya ranar Laraba domin yanke hukunci kan karar da jam’iyyar APC ta shigar na kalubalantar nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.
Aminiya ta ruwaito cewa, kotun ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da ta fitar a Yammacin wannan Litinin din.
- Majalisar Kano za ta karrama matashin da ya dawo da N15m da ya tsinta
- Tinubu ya isa New York don halartar taron Majalisar Dinkin Duniya
Sakataren kungiyar lauyoyin NNPP, Barista Bashir T/Wurzici, wanda ya tabbatar wa Aminiya, ya ce an mika wa tawagar sanarwar da yammacin ranar Litinin.
“Mun yi farin ciki ranar yanke hukunci ta zo, kuma mun yi farin ciki sosai saboda mun san za a yi watsi da kararsu.
“Muna fatan kotun za ta bi matakin da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta bi, saboda lamarin iri daya ne,” in ji shi.
A nasa bangaren, Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC a Kano, Shehu Maigari, ya ce “ya dace da mu bisa ga hujjojin da muka mika wa kotun, muna kyautata zaton za mu yi nasara.
“Ba ma tsoron komai saboda muna da kwarin gwiwa a kan takardun shaida da muka gabatar.
“Don haka muna da kyakkyawan fata bisa ga abin da muka gabatar.”
Aminiya ta ruwaito cewa, jiran tsammanin yanke hukunci ya haifar da rudani a jihar, inda a makonnin da suka gabata bangarorin biyu na jam’iyyun da ke adawa da juna suka shirya addu’o’in neman nasara.
A yayin da ake dakon hukuncin kotun ne kuma Gwamna Abba Kabir ya kori wanu kwamishinansa saboda yi wa alkalan kotun barazanar kisa kan zargin ba za su yanke hukuncin da ya dace ba saboda zargin cewa karbi na goro.
Lauyan jam’iyyar APC, Offiong Offiong (SAN) ya bayyana cewa, shaidun da mai shigar da kara ya gabatar a gaban kotun sun tabbatar da cewa Gwamna Yusuf ba dan jam’iyyar NNPP ba ne kafin zabe, don haka bai cancanci takara ba .
Ya kuma kara da cewa wadanda ake kara sun kasa musanta cewar akwai magudi a cikin wasu takardun zabe sama da 130,000 da aka yi amfani da su wajen bayyana Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben, kuma idan aka rage adadinsu, dan takarar APC ne zai lashe zaben.
A nasa bangaren, Lauyan Gwamna Yusuf, Adegboyega Awomolo (SAN), ya bayyana cewa dukkan shaidu 29 da mai shigar da kara ya kira, ‘yan damfara ne, kuma bai kamata kotun ta yi aiki da duk wata shaida da suka bayar ba.
Ya kara da cewa, ya kamata a ce wanda ya shigar da karar yana da wata shaida a gaban kotun yayin da lauyan NNPP ya gabatar da cewa kotun koli ta yanke hukuncin cewa wani daga waje, ba zai iya fada wa NNPP abin da za ta yi ba.
Bayan haka, shugabar kwamitin alkalan mai mutane uku, Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, ta yi alkawarin tabbatar da adalci ga dukkan bangarorin, inda ta kara da cewa hukuncin zai zo gabanin kwanaki 180 da doka ta ba da damar sauraro da tantance takardar koken da aka shigar a gabanta.