Kotu ta tura Dagacin Tudun Yola gidan maza a kan rikicin fili

Kotun Shari’ar Musulunci da ke kofar Kudu a Kano ta bayar da umarnin a tsare Dagacin Tudun Yola bisa samun hannunsa dumu-dumu a cikin rikicin filaye. Tunda farko an gurfanar da Dagacin ne saboda karar da wata mata mai suna Hafsat Mohammed ta shigar inda take da’awar cewa ta sayi fili a hannun Dagacin tare […]

Kotu ta tura Dagacin Tudun Yola gidan maza a kan rikicin fili
Kotu ta tura Dagacin Tudun Yola gidan maza a kan rikicin fili

Kotun Shari’ar Musulunci da ke kofar Kudu a Kano ta bayar da umarnin a tsare Dagacin Tudun Yola bisa samun hannunsa dumu-dumu a cikin rikicin filaye. Tunda farko an gurfanar da Dagacin ne saboda karar da wata mata mai suna Hafsat Mohammed ta shigar inda take da’awar cewa ta sayi fili a hannun Dagacin tare da damka masa amanar filin tsawon shekara 12 da suka wuce. Matar ta shaida wa kotu cewa lokacin da ta tuntubi Dagacin kan batun filin nata sai ya canja mata da wani filin, inda daga baya ta gano cewa ba nasa ba ne. Yayin da kotu ta waiwaye Dagacin Tudun Yola, Malam Hamisu Nasidi ya musanta wannan da’awa inda ya bayyana wa kotu cewa bai san da wannan magana ba. Sai dai da kotu ta tsananta bincike sai aka gano wata yarjejeniya da suka taba kullawa tsakanin mutanen biyu inda shi Dagacin ya ba Hafsa Naira dubu 45. Alkalin Kotun Atiku Mohammad Bello ya ce akwai kanshin gaskiya a cikin da’awar matar, don haka ya bayar da umarnin A tsare Dagacin tare da dage shari’ar zuwa nan gaba.