Kotu ta tura kansila kurkuku kan batanci ga Gwamnan Jigawa

Wata Kotun Majistare da ke Dutse a karkashin jagorancin Mai shari’a Tijjani Garba Ringim ta tura  wani kansila mai suna Aliyu Magaji gidan maza bisa zarginsa da yin maganganun batanci a kan Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar.Kotun ta tura kansilan zama wakafi ne a gidan yarin Dutse zuwa yau Juma’a da za a […]

Kotu ta tura kansila kurkuku kan batanci ga Gwamnan Jigawa
Kotu ta tura kansila kurkuku kan batanci ga Gwamnan Jigawa

Wata Kotun Majistare da ke Dutse a karkashin jagorancin Mai shari’a Tijjani Garba Ringim ta tura  wani kansila mai suna Aliyu Magaji gidan maza bisa zarginsa da yin maganganun batanci a kan Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar.
Kotun ta tura kansilan zama wakafi ne a gidan yarin Dutse zuwa yau Juma’a da za a ci gaba da shari’arsa, bayan da ’yan sanda suka kama shi a ranar Litinin da yamma, inda suka gabatar da shi a gaban kotun a ranar Talatar da ta gabata Da yake amsa tanbayoyin alkalin kotun, wanda ake tuhumar bai yi musun abin da ake tuhumarsa ba na cewa ya yi kalaman batanci a gidan rediyon Freedom a wani shiri da ake cewa ‘Baki Ke Yanka Wuya.’
Alkalin Kotun ya ki ba da beli ga wanda ake tuhumar kamar yadda lauyansa ya nema, ana tuhumar kansilan ne a karkashin sashi na 393 na manyan laifuffuka na dokokin shari’a.
Kansila Magaji Aliyu wanda ya fito daga karamar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa ya shiga gidan rediyon ne yana ikirarin cewa wai Gwamna Badaru yana da Fasfo iri biyu na harkar gwamnati da kuma na kasuwanci.
Ya ce duk lokacin da Gwamnan zai fita waje to yana fita ne da bizar kasuwanci wani lokacin ma wai biza biyu yake yi in ya kammala aikin gwamnati da ya fitar da shi sai kuma ya yi amfani da bizarsa ta kasuwanci domin bunkasa harkar kasuwancinsa.
Kuma ya yi zargin cewa Gwamnan ba ya zama a jihar sai dai yawo kullum yana kasashen waje, inda ya ce daga zabansa zuwa yanzu ya fita waje har sau 19.
Sannan kansilan ya zargin Gwamnan da cewa a duk lokacin da wata tawagar gwamnoni ko ta Gwamnatin Tarayya ta fita tare da dashi ba ya dawowa jihar sai ya tsaya ya yi kasuwanci.
Bayanai sun ce wadannan zarge-zargen ne ake jin suka harzuka Gwamna Badaru ya yi karar kansilan wajen ’yan sanda yana bukatar su bi masa hakki na yi masa kazafi.
Kakakin Gwamnan Alhaji Bello Muhammad Zaki ya ce gaskiya ne su ne suka sa aka kama tsohon kansilan na PDP, Magaji Aliyu saboda kalaman batanci da ya yi a kan Gwamnan.
Ya ce daga yanzu duk wanda ya yi kalamai na batanci saboda wasu sun biya shi, ba za su saurara masa ba za su kai shi kotu domin hakan ya zama darasi ga saura.