Kotu ta tura matashin da ya yi wa tsohuwa fyade zuwa kurkuku

Bayan fyade, matashin ya yi wa tsohuwar wadda makwabciyarsu ce fashin tsabar kudi da wayar hannu.

Kotu ta tura matashin da ya yi wa tsohuwa fyade zuwa kurkuku

Kotu

Wata kotun Majistare mai zamanta a yankin Iyaganku na Ibadan, Jihar Oyo, ta tura wani matashi zuwa gidan yari kan zargin yi wa wata tsohuwa ’yar shekara 70 da suke makwabta fyade.

Tun farko, mai tuhuma, Sufeta Femi Oluwadare, ya fada wa kotun cewa, ana zargin matashin da aikata wa tsohuwar fayade da fashin kudi N21,500 da wayar salula ta N6,000a a wani kango a ranar 6 ga Oktoba.

Ya ce laifin ya saba wa Sashe na na 357 wanda hukuncinsa ke karkashin Sashe na 358 na kundin Dokokin Mayan Laifuka na Jihar Oyo na 2000.

Ba tare da sauraron rokon da ya yi wa kotun ba, alkali Emmanuel Idowu, ya ba da umarni a kai matashin a ajiye a Gidan Gyaran Hali da ke Abolongo a birnin Oyo.

Matashin zai ci gaba da zaman kurkun ne har zuwa lokacin da kotu ta samu bayanai kan batunsa daga sashen gabatar da kararraki na jihar.

Alkalin ya dage ci gaba da shari’ar ya zuwa 15 ga Disamba mai zuwa.