Kotu ta tura wanda ya kona masallata a Kano zuwa gidan yari

Shafi’u ya amsa laifinsa a gaban alkali, amma dage shari’ar zuwa ranar 31 ga watan nan na Mayu, 2024

Kotu ta tura wanda ya kona masallata a Kano zuwa gidan yari

Babbar Kotun Shariar Musulunci da ke zamanta a Rijiyar Zaki a Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare mutumin nan da ake zargi da cinna wa wasu mutane wuta a yayin da suke sallah a garin Larabar Abasawa a yankin Karamar Hukumar Gezawa.

Mai gabatar da kara, Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Sharia, Barista Haruna Isa Dederi, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargi mai suna Shafiu Abubakar Gadan, ya zuba man fetur sannan ya cinna wuta a kan wasu mutane da ke yin sallar asuba a jam’i a masallacin da ke garin Gadan a yankin Karamar Hukumar Gezawa, lamarin da ya janyo da yawa daga cikin masallatan suka kone yayin da wasu suka mutu.

Bayan karanto masa takardar tuhumarsa, wanda ake zargin ya amsa aikata laifukan da ake zargin sa da shi na barna da samar da mummunan rauni da kisan kai bisa ganganci.

Sai dai lauyoyi sun nemi a sama wa wanda ake tuhumar lauyan da zai kare shi.

Alkalin kotun, Mai Sharia Halhalatulhuza’i Zakariyya, ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 31 ga watan Mayu, 2024 don sake gurfanar da shi.

Haka kuma alkalin ya amince da a sama wa wanda ake tuhumar lauyan da zai ba shi kariya duba da girman laifin da ake tuhumar sa da shi wanda idan ya tabbata hukuncinsa shi ne kisa.

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai