Yahaya Bello zai yi bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara a gidan Yari
Kotu ta tura tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello zuwa Gidan Yarin Kuje kan almundahanar Naira biliyan 110.4.
Kotu ta tura tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello zuwa Gidan Yarin Kuje kan almundahanar Naira biliyan 110.4.
A ranar Talata Mai Sharia Maryann Anenih ta bayar da umarnin tare da dage sauraron shari’ar zuwa ranar 29 da watan Janairun 2025.
Umarnin na zuwa ne bayan Hukumar Yaki da Masu Karyta Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) ta kama tsohon gwamnan wanda suka jima suna wasan buya da shi.
Tun da farko alkalin ta yi watsi da neman belin Yahaya Bello, wanda ta ce an yi riga malam masallaci, saboda an shigar da bukatar ce kafin a kama shi ko a gurfanar das hi a kotu, don haka ba ta da amfani.
- Dan Jam’iyyar LP a Majalisar Tarayya ya sauya sheka zuwa APC
- Me Tinubu ya yi da za a sake zaben shi —Atiku
- An yi garkuwa da hadimin Yahaya Bello
Ta ci gaba da cewa, “Shi ma bukatar belin da aka shigar nan take ya yi riga malam masallaci, don haka ba a amince da shi ba.”
Yahaya Bello da wasu mutum biyu dai suna fuskantar shari’a ne kan zargin karkatar dan Naira biliyan 110.4 a lokacin da yake Gwamnan Jihar Kogi.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da su tana tuhumar su da laifuka 16 tare da jami’an gwamnatin nasa, Abdulsalami Hudu da kuma Umar Oricha wadanda ake zargi da hada baki da kuma mallakar gidaje a unguwannin masu kudi a Abuja da birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da kudinsu ya kai biliyan N110.4.