Kotu ta tura ’yan TikTok gidan yari a Kano
Wadanda kotun ta tura zuwa gidan yarin sun hada da Idris Mai Wushirya, Aminu BBC da kuma Sadiq Shehu Shariff
Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Filin Hockey a Kano ta tura matasa masu tashe a TikTok ciki har da Murja Ibrahim Kunya zuwa gidan yari.
Ragowar wadanda kotun ta tisa keyarsu zuwa gidan yarin sun hada da babban abokin Murja Kunya, wato Idris Mai Wushirya, Aminu BBC da kuma Sadiq Shehu Shariff wanda ya yi wakar ‘A Daidaita’.
- Mutum 4 sun mutu a zanga-zangar karancin kudi a Edo
- Kotu ta tsare matashi kan luwadi da karamin yaro a Kaduna
Hakan kuwa na zuwa ne a yayin da ita Murja take cika mako biyu da zaman wakafi a gidan yari, a wata shari’a ta daban a gaban kotun.
A zaman kotun na ranar Alhamis ne Mai Shari’a Abdullahi Halliru, ya ba da umarnin tisa keyar masu amfani da TikTok din zuwa gidan yari.
Kotun ta tura su zaman wakafin na tsawon mako guda ne a shari’ar da zauren malaman Kano ta maka matasan kan zargin wallafa bidiyon batsa a TikTok.
Ana zargin Murja da abonkan nata ne da laifin yada batsa da kuma lalata tarbiya a TikTok, amma sun musanta zargin, in banda Aminu BBC da Mai Wushirya da suka amsa.
Amma a kunshin tuhumar da mai gabatar da kara, Lamido Abba Sorondinki, ya karanto a gaban kotun, an zargi Sadik Sharif Umar zargin da yin wasu wakoki masu dauke da kalaman batsa da lalata tarbiyar yara.
Sai dai ya amsa cewa shi ya yi wakar, amma musanta zargin da ake yi masa na yin wakar batsa.
Mai gabatar da kara ya roki kotun ta yi mu su hukunci nan take amma lauyansu ya roki kotun ta ba da belinsu.
Alkalin kotun ya bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali har zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu 2023 domin dawo da su gaban kotun.