Kotu ta umarci Atiku ya ba wa tsohuwar matarsa ’ya’yanta

Ta ce Abubakar Atiku ya gaza gamsar da ita dalilinsa na hana Maryam Sharif rike ’ya’yanta

Kotu ta umarci Atiku ya ba wa tsohuwar matarsa ’ya’yanta

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, mahaifin wanda ake kara.

Wata Babbar Kotu a Abuja ta bai wa Alhaji Abubakar Atiku umarnin bai wa matar da ya saka ’ya’yanta maza uku domin su kasance a karkashin kulawarta.

A bara ne matar mai suna Maryam Sharif ta yi karar Abubakar Atiku, dan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP a shakarar 2015, Atiku Abubakar, tana bukatar kotun ta maido mata da ’ya’yanta uku.

Daga baya aka dauke karar daga Babbar Kotun da ke Gudu zuwa wadda ke Kubwa domin ci gaba da shari’a.

A lokacin da yake yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a Bashir Danmaisule ya cw wanda ake karar ya gaza ba da hujjar hana tsohuwar matar tasa rike ’ya’yanta kamar yadda tsarin Musulumci ya tanada.

Sai dai ya ce wanda aka yi karar na da damar daukaka kara cikin kwana 30 da yanke hukuncin.

Kotun ta karbi shaidu biyar da karar, Maryam Sharif ta gabatar tare da lauyanta, Nasir Sa’idu a lokacin zaman.

A daya bangaren wanda ake karar Abubakar Atiku da lauyansa Abdullahi Hassan ba su halarci zaman kotun ba.

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano