Kotu ta umarci Jami’ar Bayero ta mayar da malami bakin aikinsa
Kotun Harkokin Ma’aikta da ke Kano ta soke korar da Hukumar Jami’ar Bayero Kano ta yi ga wani malamin jami’ar Dokta Aminu Audu Bichi, inda ta ce jami’ar ba ta bi ka’idojin korar aiki ba a lokacin da ta kore shi a shekarar 2012. Kotun ta zargi Jami’ar ta Bayero da gazawa wajen kawo wa […]
Kotun Harkokin Ma’aikta da ke Kano ta soke korar da Hukumar Jami’ar Bayero Kano ta yi ga wani malamin jami’ar Dokta Aminu Audu Bichi, inda ta ce jami’ar ba ta bi ka’idojin korar aiki ba a lokacin da ta kore shi a shekarar 2012. Kotun ta zargi Jami’ar ta Bayero da gazawa wajen kawo wa kotun shaidun da za su tabbatar da zargin da take yi wa malamin na cewa malamin na yin wasu ayyuka da suka jawo bata suna ga jami’ar. Alkalin Kotun Mai shari’a Lawal Mani ya umarci hukommin jami’ar su mayar da malamin bakin aikinsa ba tare da wani bata lokaci ba, kuma su biya malamin dukkan hakkokinsa tun daga albashi zuwa alawus-alawus cikin kwanaki 30 da yanke hukuncin. Kotun ta kuma ce dole jami’ar ta samar wa malamin ’yanci da walwala kamar kowane malami a jami’ar. Idan za a iya tunawa a kwankin baya kotun ta yanke irin wannan hukunci a kan jami’ar kan korar wasu leburorinta, hukuncin da jami’ar ta yi gaggawar bi inda ta mayar da su bakin aikinsu.