Kotu ta umarci likitoci su koma bakin aiki nan take

Kotu ta umarci likitoci su janye yajin aikin da suka shiga su ceci rayuka.

Kotu ta umarci likitoci su koma bakin aiki nan take

Likitan Najeriya

Wata kotun ma’aikata da ke zamanta a Abuja ta umarci likitoci  masu namen kwarewa da su janye yajin aiki su koma bakin aikinsu nan take.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Bashir Alkali, shi ne ya yanke hukunci cewa dole likitocin sun koma bakin aiki don ceto rayukan al’umma, wadanda annobar COVID-19 ke yi wa barazana.

Umarnin kotun ya biyo bayan karar Kungiyar Likitoci Mas Neman Kwarewa (NARD) da Gwamnatin Tarayya ta shigar ta hannun Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya.

Bayani na tafe…