Kotu ta umarci Mandla ya mayar da gawarwakin ’ya’yan Mandela kauyen kunu

Babbar Koun Eastern Cape da ke kasar Afirka a Kudu a umarci Mista Mandla Mandela wani jikan tsohon Shugaban kasar Mista Nelson Mandela da ke kwance a asibiti rai kwakwai-mutu-kwakwai cewa ya mayar da gawarwakin ’ya’yan Mandelan zuwa kunu domin sake binne su a can. Alkalin Kotun Lusindiso Pakade ne ya yanke hukunci a shekaranjiya Laraba […]

Kotu ta umarci Mandla ya mayar da gawarwakin ’ya’yan Mandela kauyen kunu
Kotu ta umarci Mandla ya mayar da gawarwakin ’ya’yan Mandela kauyen kunu

Babbar Koun Eastern Cape da ke kasar Afirka a Kudu a umarci Mista Mandla Mandela wani jikan tsohon Shugaban kasar Mista Nelson Mandela da ke kwance a asibiti rai kwakwai-mutu-kwakwai cewa ya mayar da gawarwakin ’ya’yan Mandelan zuwa kunu domin sake binne su a can.
 Alkalin Kotun Lusindiso Pakade ne ya yanke hukunci a shekaranjiya Laraba bayan Mandla jikan Madiba kamar yadda ake kiran Mandela kuma sarkin mahaifarsa Mbezo ya kalubalanci umarnin da aka ba shi na dawo da gawarwakin. Ya tone gawarwakin ne daga kaburburansu da ke kunu zuwa Mbezo a shekarar 2011 ba tare da sani ko shawartar sauran danginsa ba.
Kotun ta bayar da zuwa karfe 3:00 na yammacin Larabar a sake ciro gawarwakin don maida su makwancinsu na farko.
A makon jiya ne kotun ta fara bayar da wannan umarni bayan da 16 daga cikin iyalan Mandela ciki har da babbar ’yarsa Makaziwe Mandela, suka bukaci a gaggauta tilasta Mandla ya mayar da gawarwakin.
Makaziwe Mandela da dan kanenta Ndaba Mandela da kuma ’yar kanenta Ndileka Mandela duk suna kotun a ranar Laraba domin jin yadda shari’ar za ta kaya.
Kaburburan sun hada da na babban dan Mandela kuma mahaifin Mandla, Mista Makgatho Mandela, wanda ya mutu a shekarar 2005 da babbar ’yar Mandela mai suna Makaziwe Mandela wadda tana jaririya a 1948 da kuma dan Mandela na biyu Madiba Thembekile,  wanda ya mutu a hadarin mota a 1969.