Kotu ta umarci matashi ya biya wadda ya ajiye diyya kan bata mata rayuwa

Wata Kotun Majistire da ke garin Masaka a karamar Hukumar Karu a Jihar Nassarawa, ta umurci wani matashi mai suna Ibrahim danliti da ya biya diyya ga wata yarinya da ya ajiye a gidansa na tsawon lokaci ba tare da aure a tsakaninsu ba, bayan kotun ta same shi da laifin bata mata rayuwa. karar […]

Kotu ta umarci matashi ya biya wadda ya ajiye diyya kan bata mata rayuwa

Wata Kotun Majistire da ke garin Masaka a karamar Hukumar Karu a Jihar Nassarawa, ta umurci wani matashi mai suna Ibrahim danliti da ya biya diyya ga wata yarinya da ya ajiye a gidansa na tsawon lokaci ba tare da aure a tsakaninsu ba, bayan kotun ta same shi da laifin bata mata rayuwa.

karar wadda tun farko matashin ne ya shigar da ita kan zargin yarinyar tare da wasu danginta uku da aikata laifukan hada kai wajen aikata lafi da tursasawa da tilasta masa ba da kudi da cin zarafi da kuma nuna karfi, wanda lafuffuka ne da suka saba da dokoki na 96, da 396, 291, da 264, da kuma 263 a tsarin dokoki na Finalkod.

Hukuncin kotun ya biyo bayan sauraron bahasin wadda ake karar, mai suna kueen Faith Emmanuel a yayin zaman kotun a ranar Litinin da ta gabata, inda ta sanar da kotun cewa wanda yake karar, wanda dan asalin Kudancin Jihar Kaduna ne da ya fara haduwa da ita a shagon sayar da abincin mahaifiyarta da ke Unguwar Jabi daki biyu a Abuja, ya yaudare ta, inda a sakamakon hakan ta rika tarewa gidan da yake da zama a garin Masaka a ranakun karshen mako tun daga shekara ta 2013 kafin a karshe ta koma wajensa dungurugum a shekara ta 2017, bayan sana’ar da take yi ta dakata.

Ta ce sai dai wanda ke karar nata ya daura mata karan tsana, tun bayan lokacin da ta sanar da shi cewa ta samu ciki a farkon wannan shekarar sannan bayan ya musanta cewa nasa ne, ta kai maganar cocinsa, inda aka yi gwaji aka tabbatar cewa nasa ne. Ta ce cikin ya zube daga bisani.

Ibrahim danliti, wanda bai musanta bayanan nata ba, ya zargi dangin yarinyar da yunkurin tilasta masa aurenta bayan sun gayyace shi zuwa kauyenta da ke kusa da garin Akwanga, Jihar Nassarawa, inda a cewarsa suka yi masa barazana tare da cin zarafinsa da kuma karbar Naira dubu 11 daga wajensa a matsayin somin tabin kudin kulla aure.

A shari’ar da ya yanke, Alkalin B. B. Manga, ya umarci saurayin da ya yi zaman sulhu da dangin yarinyar tare da tattaunawa a kan adadin diyyar da zai biya ta, bayan kotun ta same shi da aikata laifin bata mata rayuwa, ya bukaci da su dawo kotun bayan mako biyu.