Kotu ta umarci Shugaba Mugabe ya gudanar da zabe kafin Agusta

Babbar kotu a kasar Zimbabwe ta umarci Shugaban kasar Robert Mugabe ya gudanar da zabe kafin watan Agusta mai zuwa.Alkalin babbar kotun Godfrey Chidyausiku ne ya ba Mugabe umarnin gudanar zaben shugaban kasa da na majalisa da kuma sauran zabubbuka a yayin zaman kotun a ranar Juma’ar da ta gabata.Ya ce: “Kotu ta ba Shugaba […]

Kotu ta umarci Shugaba Mugabe ya gudanar da zabe kafin Agusta
Kotu ta umarci Shugaba Mugabe ya gudanar da zabe kafin Agusta

Babbar kotu a kasar Zimbabwe ta umarci Shugaban kasar Robert Mugabe ya gudanar da zabe kafin watan Agusta mai zuwa.
Alkalin babbar kotun Godfrey Chidyausiku ne ya ba Mugabe umarnin gudanar zaben shugaban kasa da na majalisa da kuma sauran zabubbuka a yayin zaman kotun a ranar Juma’ar da ta gabata.
Ya ce: “Kotu ta ba Shugaba Mugabe umarnin gudanar da zabe kafin watan Agusta mai zuwa, wato yana da damar gudanar da zaben har zuwa 31 ga watan Yuli, 2013.”
Ofishin Firayiminista Morgan Tsbangirai ya ce umarnin da kotu ta bayar ya wuce makadi da rawa.
Tun kafin wannan lokaci Mugabe yake so ya gudanar da zabe, amma kuma bangaren Tsbangirai ya nuna adawa kan hakan inda yake bukatar a gudanar da wadansu shirye-shirye da tsare-tsare kafin a gudanar da zaben.
Mai magana da yawun firayiminista Tsbangari Luke Tamborinyoka ya ce “Wannan umarnin da kotu ta bayar ya wuce makadi rawa. Babu wata kotu da take da ikon sanya lokacin zabe; bangaren zartarwa ne ke da wannan ikon.”
Sabon kundin tsarin mulkin kasar ya yi umarnin a gudanar da zabe wata hudu bayan an rushe majalisar dokoki.
Mawarire ya ce rashin gudanar da zaben a yanzu zai sanya Mugabe ya rika mulki shi kadai hakan kuma cin fuska ne ga dimokuradiyya.