Kotu ta umarci sojoji su kawo Sheikh Sani Khalifa Zaria 

Babbar Kotun Tarayya umarci Hukumar Leken Asiri ta Soja (DIA) da ta kawo malamin Musulunci nan da hukumar take tsare da shi, Sheikh Sani Abdulkadir Zariya.

Kotu ta umarci sojoji su kawo Sheikh Sani Khalifa Zaria 

Babbar Kotun Tarayya umarci Hukumar Leken Asiri ta Soja (DIA) da ta kawo malamin Musulunci nan da hukumar take tsare da shi, Sheikh Sani Abdulkadir Zariya.

Dama da wata biyu ke nan DIA tana tsare da Sheikh Sani Khalifa kan  zargi fa ta kira alaƙa da yunƙurin juyin mulki ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a ranar 1 ga watan Oktoba, 2025.

Kotun ta bayar da wannan umarni ne a bayan lauyoyin malamin, Sunusi Musa (SAN), Abdul Aliyu (SAN), da Mohammed Sheriff sun shigar da ƙarar neman ’yancin Sheikh Zariya, ibda inda suka shigar da EFCC, DIA, Ministan Shari’a na Tarayya, da kuma Jaiz Bank Plc a matsayin waɗanda ake ƙara

Alkalin kotun, Mai Shari’a Peter Lifu, ya bayyana cewa dukkan hukumomi suna ƙarƙashin ikon farar hula, domin Najeriya tana karkashin mulkin dimokuraɗiyya. Ya ce kundin tsarin mulkin ƙasar na 1999, musamman sashe na 36 (1)(5)(6), ya ba da kariya ga dukkan ’yan ƙasa.

A zaman da aka yi a ranar Alhamis, kotun ta umurci DIA da ta gabatar da malamin ko kuma ta nuna hujjar doka da ta dogara da ita wajen ci gaba da tsare shi.

Lauyan DIA, I. O. Odom, ya shaida wa kotu cewa ana tsare da malamin ne a madadin Hedikwatar Tsaro, inda ya ƙara da cewa shugaban kwamitin bincike na musamman ya fita ƙasar.

Iyalan malamin sun danganta matsalar malamin da wata kyauta ta Naira miliyan biyu da aka tura wa asusun bankinsa, wanda aka danganta da wani daga ciki waɗanda ake zargi da yunƙurin juyin mulki.

Alkalin kotun ya kuma nuna cewa tun daga 11 ga Disamba, 2025, ana tsare da malamin ba tare da samun damar ganin iyalansa da abokansa ba, bisa dalilan tsaro.