Kotu ta ummarci bankin Zaneth ya biya lauya hakkinsa daga asusun PDP
Mai Shari’a Oluwatoyin Ipaye ta Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas ta bayar da ummarnin da zai tilasta wa bankin Zenith ya biya wani lauya mai suna Debo Adeleke Naira miliyan 10 da dubu 500 daga asusun ajiyar jam’iyyar PDP. Umarnin alkalin ya biyo bayan kin yarda da jam’iyyar PDP ta yi ta biya […]
Mai Shari’a Oluwatoyin Ipaye ta Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas ta bayar da ummarnin da zai tilasta wa bankin Zenith ya biya wani lauya mai suna Debo Adeleke Naira miliyan 10 da dubu 500 daga asusun ajiyar jam’iyyar PDP.
Umarnin alkalin ya biyo bayan kin yarda da jam’iyyar PDP ta yi ta biya lauyan kudin bayan da ya yanke hukuncin da ya bai wa lauyan nasara a kan jam’iyyar.
Da yake yanke hukunci a kan lamarin, mai shari’a Ipaya ta yi watsi da hujjojin da jam’iyyar ta bayar na kin biyan kudin. Saboda haka sai alkalin ta ummarci bankin Zeneth ya bayar da cakin kudin ga lauya Adeleke a cikin kwanaki uku.
Mai shari’a Ipaye ta yi takaicin yadda har sai lauya ya kai wanda ya yi wa aiki kotu domin ya biya shi hakkinsa.
Lauya Adeleke ya maka hedikwatar jam’iyyar ta kasa da reshen jam’iyyar da ke Jihar Legas a kotu kan rashin biyansa basussukan da yake bin su na aikin da ya yi musu, inda ya wakilce su har sau 180 a kotu.
Lauya Adeleke ya bayyana cewa ya wakilci jam’iyyar a shari’o’in zabe daban-daban har guda bakwai a matakin karamar hukuma a kotunan jin kararakin zabe, tun daga watan Nuwanban 2011 zuwa watan Agustan 2012, amma sai jam’iyyar ta ba shi miliyan daya da dubu 45 daga cikin miliyan 12 da aka yi yarjejeniya.