Kotu ta umurci ’yan sanda su biya shi N1m saboda tsare shi ba bisa ka’ida ba

Kotun ta ce tsare shin take hakkinsa na dan Adam.

Kotu ta umurci ’yan sanda su biya shi N1m saboda tsare shi ba bisa ka’ida ba

Kotu

Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja a Jihar Kogi a ranar Talata ta umarci ’yan sanda da su biya diyyar Naira miliyan daya ga wani wanda suka tsare ba bisa ka’ida ba, saboda takle hakkinsa na dan Adam.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Sunday Bassay-Onu, ne ya ba da umarnin a yayin gabatar da shari’ar da Daniel Atabor ya shigar, ta hanyar lauyansa, Mr O.E Amoke.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ’yan sanda sun kama Atabor ne a ranar 25 ga watan Satumba a Lokoja kan tuhumar siyan mashin din sata daga wajen wani mutum.

Daga nan ne suka ajiye shi a wajensu ba tare da ba da beli ba ko shigar da kara.

Mai Shari’a Bassay-Onu ya bayyana ci gaba da tsare shi a matsayin keta hakkinsa hadi da watsi da sashe na hudu na kundin aikin dan sanda, wanda ya hana ajiye wanda ake zargi fiye da kwana biyu.

“Dangane da ajiye mai kara fiye da lokacin da kundin aikin ’yan sanda ya yi nuni, an keta hakkin shi kamar yadda sassa na 34, 35(1)(3)(4)(5)(6), 37 da na 41(1)(2) na Kundin Tsarin Mulki na 1999, wanda aka yi wa kwaskwarima.

“Saboda haka, kotu ta bayar da umarnin biyan kudi Naira miliyan daya ga wadanda ake kara (’yan sanda) su ba mai kara saboda keta ma shi hakki da suka yi.”

Kotun ta kuma umarci ’yan sandan su ba shi hakuri a jaridar kasa.

Tun da farko dai Atabor , ta hanyar lauyansa, ya nemi kotun da su sanar da ci gababa da rike shi da ’yan sanda suka yi a matsayin keta hakkin dan Adam, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki na 1999.

Ya kuma bukaci naira miliyan hamsin na batanci da akayi mashi ta hanyar kama shi da tsare shi da akayi fiye da awa 48 na kundin aikin yan sanda da kuma sashe na 34, 35(1)(3)(4)(5)(6), 37 da 41(1)(2) na tsarin mulki na 1999 na kasa (bayan gyara). (NAN)