Kotu ta wanke dan sandan da aka zarga da lalata da yara
Babban Kotun Jihar Bauchi ta 9 ta wanke wani dan sanda mai suna ASP Yusuf Ibrahim wanda ake zargi da lalata da kananan yara a cikin shagonsa da ke Unguwar Bakin Kura a garin Bauchi, inda kotun ta ce bai aikata laifin da ake zarginsa ba don haka ta ba da umarni a sake shi […]
Babban Kotun Jihar Bauchi ta 9 ta wanke wani dan sanda mai suna ASP Yusuf Ibrahim wanda ake zargi da lalata da kananan yara a cikin shagonsa da ke Unguwar Bakin Kura a garin Bauchi, inda kotun ta ce bai aikata laifin da ake zarginsa ba don haka ta ba da umarni a sake shi nan take.
Alkalin Kotun Mai shari’a Mu’azu Abubakar ya bayyana cewa wannan kara ce da Sabo Turaki ya shigar a gaban kotun inda yake zargin ASP Yusuf Ibrahim da lalata da ’ya’yansa (an sakaye sunansu) a shagonsa da ke Unguwar Bakin Kura a Bauchi.
Yaran masu shekara biyar da shida a duniya, an yi zargin ASP Yusuf Ibrahim ya ba su minti daga bisani ya yi lalata da su a cikin shagonsa, sai dai dukkan yara mata biyun sun bayyana wa kotu cewa duk abubuwan da suka fada an kitsa musu ne.
Mai karar Sabo Turaki ya bayyana wa kotun cewa duk abubuwan da ya fada matarsa ce ta ba shi labari cewa an yi lalata da ’yarsa a cikin wani shago da ke unguwar.
Alkalin Kotun ya kara da cewa binciken da kotun ta gudanar ta gano cewa ASP Yusuf Ibrahim bai aikata laifin komai ba, don haka ta yi watsi da wannan shari’a.
Kotu ta gayyaci likitan da ya duba lafiyar yaran inda ya tabbatar wa kotu cewa babu wata alama da ta nuna cewa an yi lalata da yaran a lokacin da ya duba lafiyarsu kuma kotun ta amince da shaidar da ya bayar.
ASP Yusuf Ibrahim yana aiki ne a hedkwatar ’yan sandan Jihar Bauchi kuma ya shafe shekara daya da wata uku a gidan yari kan wannan zargi kuma yana da ’ya’ya 11.
Ya shekara 35 yana aikin dan sanda kuma ya rage saura kwana 17 ya yi ritaya aka gurfanar da shi a gaban kotun kuma ya yi aiki a jihohi da dama na kasar nan.
Umar Sarki shi ne lauyan ASP Yusuf Ibrahim ya bayyana gamsuwa da hukuncin kotun.
Da yake zantawa da Aminiya a wajen kotun dan wanda aka wanken Alhaji Kamalu Yusuf Ibrahim ya ce sun gode wa Allah kuma sun gode wa daukacin wadanda suka rika yi musu addu’o’i kuma ga shi Allah Ya barrantar da mahaifinsu kotu ta wanke shi daga zargin da aka yi masa. “Nan da kwanaki kadan za mu duba ko za mu nemi diyyar bata masa suna da aka yi da zarar mun kammala tattaunawa zan yi karin bayani gare ku,” inji Kamalu.
A ranar Alhamis din makon jiya ne kotun ta yanke wannan hukunci.