Kotu ta wanke Hajiya Amart kan zargin hukumar tace fina-finai
Kotu ta yi watsi da ƙarar, inda ta ce ba a shigar da ƙarar bisa ƙa’ida.
Wata Babbar Kotu mai lamba 25 da ke Jihar Kano, ta kori ƙarar da Hukumar Tace Fina-finai ta jihar, ta shigar kan fitacciyar furodusa Hajiya Aishat Tijjani, wadda aka fi sani da Hajiya Amart.
Hukumar tace fina-finai ta zargi Hajiya Amart da shirya fina-finai ba tare da lasisi ba, kuma ta nemi kotu ta yanke mata hukunci.
- Yadda muka fatattaki ’yan bindiga daga dajin Kano — Ganduje
- Gobara ta ƙone shaguna da kadarori a kasuwar Edo
A baya, hukumar ta ƙwace lasisin wasu kamfanonin fina-finai biyu mallakin Hajiya Amart, wanda ya hana ta tallata ko kasuwancin fina-finanta a Kano.
Sai dai Babbar Kotun ta yi fatali da ƙarar, inda ta ce ba huruminta ba ne kuma ba bisa doka aka shigar da ƙarar ba.
Tun a ranar 13 ga watan Fabrairun 2024 ne hukumar ta nemi kotun majistare mai lamba 60 ta yi sammacin Hajiya Amart bisa zargin shirya fina-finai ba tare da lasisi ba.
Amma kotun daga bisani ta wanke ta daga zargin.