Kotu ta wanke matasa biyu daga zargin kisan kai

Wata Babbar Kotu da ke Dogarawa a karamar Hukumar Sabon Garin Zariya a Jihar Kaduna, ta wanke wadansu samari biyu da aka zarge da laifin hadin baki da kisan kai.  Samarin, masu suna Abdullahi Hayatu da Sunusi Aya dukansu mazauna Tudun Jukun da ke Gundumar Tukur Tukur, Zariya, Alkalin Kotun Mai shari’a Kabiru Dabo ne […]

Kotu ta wanke matasa biyu daga zargin kisan kai

Wata Babbar Kotu da ke Dogarawa a karamar Hukumar Sabon Garin Zariya a Jihar Kaduna, ta wanke wadansu samari biyu da aka zarge da laifin hadin baki da kisan kai.

 Samarin, masu suna Abdullahi Hayatu da Sunusi Aya dukansu mazauna Tudun Jukun da ke Gundumar Tukur Tukur, Zariya, Alkalin Kotun Mai shari’a Kabiru Dabo ne ya wanke su daga zargin bayan ya shafe kusan sa’o’i biyu yana karanta hukuncinsa, inda ya ce ba a samu wadanda ake zargin su biyu da laifi ba, saboda masu gabatar da kara sun kasa gabatar wa kotun gamsassun shaidu cewa wadanda ake zargin sun hada baki domin kashe wani matashi mai suna Mansur Sale da ke zaune a Tudun Jukun a shekarar 2015.

Mai shari’a Kabiru Dabo ya kara da cewa duk shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar a gaban kotun sun kasa bai wa kotun gamsassun hujjoji da za su sanya a samu wadanda ake zargin da laifi, duk kuwa da irin tambayoyi da aka yi musu domin samun cikakken bayani. 

Mai shari’a Dabo ya ce sakamakon gazawar da masu gabatar da kara suka yi na gabatar da gamsasshiyar hujja a kan matasan biyu sun aikata laifi, kotun ba ta da wani zabi illa ta sallami wadanda ake zargin.

Bayan kammala zaman kotun wadda ta cika da ’yan uwa da abokan arzikin matasan biyu, Aminiya ta zanta da lauyan matasan, Yemi Adekunle inda ya ce, “Kotu tana amfani da gamsassun hujjoji ne ba shaci- fadi ba, kuma tun daga tsayuwar mai ba da shaida ake gane mai gaskiya, don haka kotu ta yi abin da ya dace domin ta bi shari’ar daki-daki.

Matasan biyu, Abdullahi Hayatu da Sunusi Aya, dukansu Ma’aikatan kungiyar Ci gaban Masarautar Zazzau da Kula da Harkokin Tsaron Jama’a ne wato ZEMSO.