Kotu ta wanke mutum 888 daga zargin ta’addanci

Mutanen da kotu ba ta samu da kowane irin laifi ba ne kaɗai suka cancanci shirin sauya tunanin tubabbun ’yan ta’adda

Kotu ta wanke mutum 888 daga zargin ta’addanci

Tubabbun mayakan Boko Haram

Kotu ta wanke mutane 888 daga zargin ta’addanci saboda rashin hujjoji da sauran dalilai.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kotu ta wanke tare da sallamar mutanen ne bayan an gurfanar da su a cibiyar tsaron waɗanda ake zargi da aikata ta’addanci da ke Kainji a Jihar Neja.

Daraktan Gurfanarwa na Gwamnatin Tarayya, Muhammad Abubakar Babadoko, ya ce an wanke mutanen ne daga cikin rukuni shida na waɗanda ake zargi da suke tsare a cibiyar.

Ya bayyana cewa daga shekarar 2017 zuwa yanzu mutum 1,743 ne aka gurfanar a cibiyar kan zargin ta’addanci.

Babadoko ya ƙara da cewa daga cikin adadin, kotu ta yanke wa sama da mutum 200 hukunci bayan samun su da laifin ta’addanci a sassan Najeriya, sannan ta ɗage shari’o’i 92.

Ya shaida wa ’yan jarida a Abuja ranar Litinin cewa gwamnati ta ɗauki ƙwararan matakai domin taƙaita ayyukan ta’addanci a Najeriya kafin ta ci gaba da gurfanar da waɗanda ake zargin.

A nasa ɓangaren, Daraktan Shari’a na Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Sha’anin Tsaro, Zakari Mijinyawa, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka gurfanar, waɗanda kotu ba ta samu da kowane irin laifi ba ne kaɗai suka cancanci shirin sauya tunanin tubabbun ’yan ta’adda.

Tun da farko, Ko’odinetan Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ya Ƙasa, Manjo-Janar Adamu Laka, ya bayyana cewa tawagar masu ruwa da tsaki da aka zaɓo daga hukumomi da ma’aikatun gwamnati daban-daban sun taka muhimmiyar rawa wajen gurfanar da waɗanda ake zargin.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe