Kotu ta wanke Ronaldo daga zargin cin zarafin wata budurwa

A ranar Talatar da ta wuce ce wata kotu a Amurka ta wanke shahararren dan kwallon Fotugal Cristiano Ronaldo daga tuhumar da ake yi masa ta cin zarafin wata budurwa ’yar asalin Amurka Kathryn Mayorga mai kimanin shekara 35. Kathryn ta shigar da kara ce a gaban wata kotu a Amurka inda take zargin Ronaldo […]

Kotu ta wanke Ronaldo daga zargin cin zarafin wata budurwa
Kotu ta wanke Ronaldo daga zargin cin zarafin wata budurwa

A ranar Talatar da ta wuce ce wata kotu a Amurka ta wanke shahararren dan kwallon Fotugal Cristiano Ronaldo daga tuhumar da ake yi masa ta cin zarafin wata budurwa ’yar asalin Amurka Kathryn Mayorga mai kimanin shekara 35.

Kathryn ta shigar da kara ce a gaban wata kotu a Amurka inda take zargin Ronaldo da yunkurin yin lalata da ita a wani otel a Amurka a shekarar 2009 lokacin da yake yi wa kulob din Manchester United kwallo.

Budurwar ta shigar da karar ce don a bi mata kadi wajen yunkurin yin lalata da ita ba tare da amincewarta ba a wani otel a Amurka a shekarar 2009.

Sai dai a ranar Talatar da ta wuce kotun ta yi fatali da karar bisa dalilin rashin gabatar da hujjoji masu gamsarwa daga lauyoyin Kathryn, tare da wanke Ronaldo daga zargin.

A tattaunawar da aka yi da Ronaldo jim kadan bayan an kammala zaman kotun ya ce da ma budurwar ta shirya manakisa ce don ta bata masa suna ganin yadda ya yi fice a duniya a harkar kwallon kafa.

Sai dai bai bayyana ko nan gaba zai kai budurwar kara a gaban wata kotu don a hukunta ta game da wannan kazafi da ta yi masa ba.

Kathryn Mayorga dai shahararriyar ’yar kwalisa ce a Amurka inda take yi wa kamfanoni talla.