Kotu ta yanke wa Yunusa Yellow hukuncin daurin shekara 26
Wata kotun Tarayya da ke birnin Yenagoa na jiyar Bayelsa ta yanke wa Yunusa Dahiru (Yellow) hukuncin daurin shekara 26 a gidan kaso bayan samunsa da laifin safarar yara da kuma yin lalata da Ese Oruru. A shekara ta 2015 ne aka zargi Yunusa da dauke matashiyar, wacce ya ce budurwarsa ce, zuwa mahaifarsa ta […]
Wata kotun Tarayya da ke birnin Yenagoa na jiyar Bayelsa ta yanke wa Yunusa Dahiru (Yellow) hukuncin daurin shekara 26 a gidan kaso bayan samunsa da laifin safarar yara da kuma yin lalata da Ese Oruru.
A shekara ta 2015 ne aka zargi Yunusa da dauke matashiyar, wacce ya ce budurwarsa ce, zuwa mahaifarsa ta Kano, inda aka daura musu aure har ta samu ciki.
Da yake yanke hukuncin a ranar Alhamis, mai Shari’a Jane Inyang, ya wanke Yunusa daga wani zargin na yin garkuwa da matashiyar.
Sai dai alkalin, ya same shi da laifin safararta zuwa Kano da saduwa da ita da kuma yin hakan ta karfi da yaji.
Hakazalika, kotun ta daure shi shekaru biyar kan laifin safarar yara kanana, shekaru bakwai kan saduwa da ita ta karfi da yaji, shekaru bakwai kan tilasta mata mu’amala da shi, sai kuma shekaru biyar kan laifin saduwa da ita ba ta hanyar aure ba.
Alkalin ya ce Yellow zai shafe jimillar shekaru 26 a gidan kaso matukar ba wata kotun daukaka kara ce ta sauya wannan hukuncin ba.
Labarin Yunusa Yellow da Ese-Oruru dai ya janyo ce-ce-kuce sosai a Najeriya lokacin da ya fantsama a shekarar 2015.
Ita dai Ese-Oruru wacce ‘yar asalin kauyen Uwheru ce dake gundumar Ughelli a jihar Delta an yi zargin Yellow ya aure ta kana ya yi mata ciki ba tare da masaniyar mahaifanta ba.
Yayin zamanta da shi a Kano, rahotanni sun ce ta musulunta har kuma an canza sunanta zuwa Aisha kafin daga bisani ‘yan sanda a Kanon su kubutar da ita, a lokacin tana dauke da juna biyu na kusan tsawon watanni biyar da aka yi ittifakin na Yunusan ne.