Kotu ta yanke hukunci ga wadanda suka yi wa budurwa fyade

Kotun Shari’a ta daya da ke Kafanchan ta daure wasu samari hudu da ta samu da laifin yi wa budurwa fyade da ke karamar Hukumar Zangon Kataf, Jihar Kaduna. Mahaifin yarinyar, Aminu Halilu shi ne ya shigar da kara yana mai neman kotu ta bi masa hakkin bata masa yarinya da wadannan matasa suka yi […]

Kotu ta yanke hukunci ga wadanda suka yi wa budurwa fyade

Kotun Shari’a ta daya da ke Kafanchan ta daure wasu samari hudu da ta samu da laifin yi wa budurwa fyade da ke karamar Hukumar Zangon Kataf, Jihar Kaduna.

Mahaifin yarinyar, Aminu Halilu shi ne ya shigar da kara yana mai neman kotu ta bi masa hakkin bata masa yarinya da wadannan matasa suka yi da kuma biyan iyayenta kudin da suka kashe wajen jinyar ’yarsu tare da hukunta matasan.

Wadanda ake tuhuma, Huzaifa Bello da Kabiru Abdulhamid da Idris Muhammad da kuma Isma’il Muhammad, dukkansu sun amsa laifinsu a gaban shari’a, inda suka bukaci kotu da ta yi masu afuwa.

A lokacin da yake karanta hukuncin, mai shari’a Shitu Umar ya ce tun da yarinya ta tabbatar da an yi mata fyade kuma wadanda ake tuhuma sun yi ikirari bisa laifinsu, ba zai yi wu a yi masu afuwa ba, domin in da afuwa ake yi wa mai laifi to kowa ma ba zai ji tsoron aikata laifi ba saboda ya san ko an kawo shi kotu ya nemi afuwa kotu za ta karba masa, sai dai abin da ake kira rangwame.

Mai shari’ar ya zartar wa da kowannensu hukuncin biyan tarar Naira dubu 40 a matsayin sadakin tamka da kuma wasu dubu 40 a matsayin diyyar bata yarinyar, sai dubu 20 a matsayin kudin tara da kuma wasu dubu 20 a matsayin kudin jinya; inda dukkaninsu za su biya jimillar kudi Naira dubu 450 ko kuma daurin shekara shida-shida a gidan yari saboda dukkansu babu wanda ya taba yin aure a cikinsu.

Baya ga wannan hukuncin, kotu ta kuma zartar musu da hukuncin bulala 20 na ta’aziri kowannensu inda aka zartar masu da shi nan take a cikin kotun. Bayan tsare su da kwana biyu, sun biya duka kudaden inda aka sallamme su.