An yanke hukuncin sare hannun matashi kan sare hannun yaro a Gombe

Lamarin ya faru ne a ranar 12 ga watan Fabrairu, 2022, a garin Moddibo da ke Ƙaramar hukumar Yamaltu Deba, a jihar ta Gombe lokacin wani bikin aure da ya rikiɗe ya koma rikici.

An yanke hukuncin sare hannun matashi kan sare hannun yaro a Gombe

Babbar Kotun Jiha ta 5 a Gombe, ƙarƙashin Jagorancin Mai Shari’a A.M. Haruna, ta yanke wa wani matashi mai suna Abdullahi Suleiman hukuncin sare masa hannu, bisa samunsa da laifin sare hannun wani yaro mai suna Khalifa Abubakar, ɗan shekara 14 da adda.

Lamarin ya faru ne a ranar 12 ga watan Fabrairu, shekarar 2022, a garin Moddibo da ke Ƙaramar hukumar Yamaltu Deba, a jihar ta Gombe lokacin wani bikin aure da ya rikiɗe ya koma rikici da misalin ƙarfe 11 na dare yayin da angon ya kori duk wanda ke wajen saboda hayaniyar da ta kaure.

A lokacin fitar jama’a daga wajen bikin, Abdullahi Suleiman, wanda ya fito daga ƙauyen Wajari, ya yi amfani da adda wajen tarwatsa jama’a tare da wasu matasa.

Khalifa Abubakar, wanda takalminsa ya faɗi a wajen gudu, ya tsaya don ɗauka, amma Abdullahi ya kai masa sara da adda har ya sare masa hannun dama gaba ɗaya.

’Yan uwan Khalifa sun gaggauta kai shi Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya da ke Gombe, inda aka masa jinya bayan sare masa hannun.

Bayan faruwar lamarin, ‘yan uwan Khalifa sun kai ƙara ofishin ‘yan sanda da ke Deba. Sai dai daga baya an ba da belin Abdullahi Suleiman. Wannan ya sa gwamnati ta shiga lamarin, inda lauyan gwamnati, Barista Y.G. Ahmad, ya shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Jiha ta 5. Karar mai lamba GM/88c / 2022

A yayin shari’ar, kotun ta saurari shaidu biyar daga ɓangaren mai ƙara, ciki har da Khalifa Abubakar, waɗanda suka tabbatar cewa Abdullahi Suleiman ne ya aikata laifin.

Daga cikin shaida uku, sun kasance shaidun gani da ido da suka tabbatar da cewa Abdullahi ne ya sari Khalifa a lokacin rikicin.

Likitan da ya duba Khalifa shi ma Kotu ta gayyato shi ya bada shaidar jinyar da ya yi masa.

A ɓangaren wanda ake kara kuwa shaidu biyu ya gabatar wa kotu amma ba su bayar da hujjoji masu ƙarfi ba. inda bayan tantance shaidun, kotu ta tabbatar da laifin da ake tuhumar Abdullahi Suleiman akai.

Bayan tabbatar da laifin, kotu ta yi la’akari da yadda Abdullahi Suleiman ya nemi afuwa tare da nuna nadama. Sai dai Lauyan sa, Y.A. Waziri, ya roƙi kotu ta amince su saya wa Khalifa hannun roba, amma kotu ta ƙi yarda da wannan roƙo.