Kotu ta yanke wa dan Gaddafi hukuncin kisa
A ranar Talatar da ta gabata ne wata kotu a kasar Libya ta yanke hukuncin kisa a kan dan marigayi Muammar Gaddafi, Saif al-Islam da wasu mutane takwas, kamar yadda kafar yada labara ta BBC ta ruwaito Wasu daga cikin mutane takwas din da kotun ta yanke wa hukuncin kisa su ne Abdallah al-Senousi, tsohon […]

A ranar Talatar da ta gabata ne wata kotu a kasar Libya ta yanke hukuncin kisa a kan dan marigayi Muammar Gaddafi, Saif al-Islam da wasu mutane takwas, kamar yadda kafar yada labara ta BBC ta ruwaito
Wasu daga cikin mutane takwas din da kotun ta yanke wa hukuncin kisa su ne Abdallah al-Senousi, tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar da Al-Baghdadi al-Mahmudi, tsohon Firamininstan kasar.
Kotun ta ce ta samu mutanen ne da aikata laifukan yaki a lokacin juyin-juya-halin da ya yi sanadiyar kifar da gwamnatin Muammar Gaddafi a shekarar 2011.
Kotun ta kuma yanke daurin shekaru da dama a kan wasu tsofaffin jami’an gwamnatin Gaddafi.
Saif al-Islam dai ba ya kotu a lokacin da aka yanke hukuncin, kodayake, ya bayar da shaida ta hanyar bidiyo.
Wasu kungiyoyin masu tayar da kayar baya ne ke ci gaba da tsare shi a garin Zintan. Kodayake, wasu masana suna ganin cewa watakila su mika shi domin ya fuskanci hukunci.