Kotu ta yanke wa fitaccen fasto hukuncin rataya a Ribas
An tuhumi Fasto din da kashe wata mata a cocinsa.
Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani fitaccen Fasto a Jihar Ribas, Chidiebere Okoroafor, bisa samun sa da laifin kashe shugabar mawakan cocinsa.
Okoroafor, wanda kotun ta kama da laifin kashe zabiyar kungiyar mawakansa, Orlunma Nwagba, shi ne jagoran cocin ‘Altar of Solution and Healing Assembly’ da ke Karamar Hukumar Oyigbo a jihar.
- DAGA LARABA: Yadda Cire Tallafin Mai Ya Shafi Rayuwar ’Yan Najeriya
- Muhimman abubuwa 10 da Gwamnan Kano ya aiwatar a kwana 10 na mulkinsa
Kazalika, yana fuskantar karin tuhume-tuhume na kisan kai da suka shafi mutuwar kawar Nwagba, Chigozie Ezenwa, da jaririnta, Cresabel.
Da yake yanke hukunci a zaman kotun da ke Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas, Mai Shari’a Stanley Benson ya ce masu gabatar da kara sun gabatar wa kotun tabbatattun hujjoji cewa shi ya kashe wadda ake karar sa a kanta.
Daga nan sai alkali ya ba da umarnin kashe shi ta hanyar rataya.
Matan da suka rasu an zargi sun ziyarci Faston ne a gidansa wanda a nan ne ya kashe su.
Yayin da yake magana da manema labarai jim kadan bayan fitowa daga kotun, lauyan mai shigar da kara – wadda ta fito daga ma’aikatar shari’a ta jihar – Precious Ordu ta yaba da hukuncin.
Ta yaba wa kungiyar lauyoyi mata ta kasa da kasa bisa yadda suka bayar da gudunmawarsu har aka yanke da hukunci.
A nasa bangaren, lauyan wanda ake kara, Dokta Innocent Ekpu, ya ce za su daukaka kara saboda kotu ta yi kuskure wajen yanke hukunci kan wanda yake karewa.