Kotu ta yanke wa mahaifin da ya yi wa ’yarsa ciki hukuncin daurin rai da rai

Mai shari’a Blessing Egwu ce, ta yanke hukuncin ne a ranar Laraba.

Kotu ta yanke wa mahaifin da ya yi wa ’yarsa ciki hukuncin daurin rai da rai

Wata Babbar Kotu da ke Kalaba a Jihar Kuros Riba, ta yanke wa wani magidanci mai suna Imeh Sunday, mai shekara 46, hukuncin daurin rai da rai bayan samun sa da laifin yi wa ’yarsa ciki ta hanyar lalata da ita.

Mai shari’a Blessing Egwu ce, ta yanke hukuncin ne a ranar Laraba, bayan kotun ta gamsu da hujjojin da aka gabatar a gabanta.

Kotun ta tabbatar da cewa Sunday ya riƙa lalata da ’yarsa, wadda aka sakaya sunanta, har lamarin ya kai ga samun ciki.

Ƙungiyar kare haƙƙin yara mai suna Basic Rights Counsel Initiative ce ta shigar da ƙarar, inda ta gabatar da shaidu da hujjoji masu gamsarwa kan laifin da ake zargin wanda ake tuhuma ya aikata.

Alƙalin, ta bayyana cewa kotu ta gamsu da shaidun da masu ƙara suka gabatar, kuma bisa haka ne aka yanke masa hukuncin zaman gidan gyaran hali har ƙarshen rayuwarsa.

Ta ce wannan hukunci zai zama darasi ga sauran masu aikata irin wannan hali.

Bayan kammala shari’ar, babban lauyan ƙungiyar kare haƙƙin yara, Barista James Ibor, ya yaba wa kotun bisa adalcin da ta yi wajen yanke hukunci.

Ya kuma yi kira ga iyaye da su riƙa kula da ’ya’yansu, musamman ’ya’ya mata, tare da lura da duk wani canji da zai iya nuna wata matsala.

Barista Ibor, ya kuma shawarci iyaye da sauran al’umma da su kiyaye amanar yara maza da mata domin kare su daga cin zarafi.