Kotu ta yanke wa mai fyade shekara 12 a Kano

Babbar kotun jiha mai lamba 4 da ke Sakatariyar Audu Bako ta yanke wawani matashi mai suna bisa samunsa da laifin yi wa wata yarinya yarshekaru biyar fyade. Tun a ranar 12ga Oktobar 2014 aka kama wananan matashi mai suna AminuAbdullahi Zage  da laifin yi wa yarinyar (wacce aka boye sunata). Alkalin Kotun Mai shari’a […]

Kotu ta yanke wa mai fyade shekara 12 a Kano

Babbar kotun jiha mai lamba 4 da ke Sakatariyar Audu Bako ta yanke wawani matashi mai suna bisa samunsa da laifin yi wa wata yarinya yarshekaru biyar fyade.

Tun a ranar 12ga Oktobar 2014 aka kama wananan matashi mai suna AminuAbdullahi Zage  da laifin yi wa yarinyar (wacce aka boye sunata).

Alkalin Kotun Mai shari’a Ahmad Tijjani Badamasi ya bayyanacewa ya gamsu da shaidar masu gabatar da kara, don haka ya bayar daumarnin tsare wanda ake zargi a kurkuku na tsawon shekaru 12.

An gurfanar da wasu matasa a kotu kan kisan matashi, inda babbar kotun jiha mai lamba 12 da ke Sakatariyar Audu Bako ta gurfanarda mutanen uku bisa zargin su da kisan wani matashi.

Tunda farko Gwamnatin Jihar Kano ce ta shigar da kara gaban kotun, indatake tuhumar matasan da suka hada da Adamu Sa’idu Mai gemu daAbdullahi Rahama da Auwalu Rahama da laifin kashe matashi AhmadMustapha, ta hanyar daura masa igiya a wuyansa, inda suka shake shi daita har ya ce ga garinku nan.

Sai daidaukacin wadanda ake zargin sun musanta laifukan da ake zarginsu da shi na hadin baki da kuma kisan kai, laifukan da suka saba dasashe na 97 da 221 a kundin Shari’a na Pinal Kod.Alkalin Kotun Mai shari’a Abdullahi Mahmud Bayero ya dagesauraren shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Disamba don ci gaba dasauraren shari’ar.

Ta yi karar mahaifinta kan kin aura mata saurayintaKotun Shari’ar Musulunci ta birni mai lamba daya da ke kofar Kudu tafara sauraren karar da wata budurwa ta shigar gabanta inda takekalubalantar mahaifinta game da kin amincewa ya aura mata saurayin datake matukar kauna.

Tunda farko budurwar mai suna Aisha Bala Muhammad ta yi kararmahaifinta Malam Bala Muhammad Inuwa inda ta shaida wa kotun cewa tabi duk hanyar da ta kamata kan mahaifin nata ya amince da saurayin datake so ta hanyar aura mata shi, amma fafur mahaifin nata ya kiamincewa.

Sai dai Malam Bala Muhammad Inuwa ya shaida wa kotun cewa bai gamsu dasaurayin da budurwar ta zabo ba, don haka a yanzu a shirye yake idanta kawo mutumin da ya dace da ita zai aura mata.

Alkalin Kotun Mai shari’a Ibrahim Sani Sarki Yola  ya dage saurarenshari’ar zuwa ranar 5 ga watan Disamba don kokarin yin sulhutsakaninsu.