Kotu ta daure masu taimakon Boko Haram shekara 10 zuwa 40 a kurkuku
Hukuncin da Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke ya hada da umarnin shigar da wasu daga cikin wadanda aka yanke wa hukunci cikin shirin gyara hali da kawar da ra’ayin ta’addanci.
Kotu
Kotu ta yanke hukuncin daurin shekara 10 zuwa shekara 40 a kurkuku ga wasu mutane da aka kama da laifin taimaka wa kungiyar Boko Haram da ISWAP, a ci gaba da shari’o’in ta’addanci da Gwamnatin Tarayya ta fara.
Hukuncin da Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke ya hada da umarnin shigar da wasu daga cikin wadanda aka yanke wa hukunci cikin shirin gyara hali da kawar da ra’ayin ta’addanci.
Shari’o’in na gudana ne karkashin jagorancin Ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, a matsayin wani bangare na dabarar gaggauta shari’o’in ta’addanci da tabbatar da adalci.
A cikin daya daga cikin hukuncin, Mai Shari’a Binta Nyako ta yanke wa Hamatu Modu hukuncin daurin shekaru 40 kan laifin samar da abinci da bayanan sirri ga ’yan Boko Haram. Kotun ta yanke masa shekaru 10 kan kowacce daga cikin tuhume hudu da ake masa, wadanda za su gudana tare.
- Sheikh Abduljabbar ya nemi kotu ta dawo da shi Kano daga Gidan Yarin Kuje
- Rikicin ADC: Wane ne Nafiu Bala?
Shehu Bukar ya samu hukuncin shekaru 20 bayan ya amsa laifin tallafa wa ayyukan ta’addanci ta hanyar satar shanu da samar da dabbobi. Kotun ta bayyana laifin a matsayin “mummuna.”
An yanke wa Isa Ali hukuncin daurin shekaru 10 bayan ya amsa laifin samar da kaya da tallafin sufuri ga ’yan ta’adda. Kotun ta kuma ce hukuncin zai fara daga ranar da aka kama shi, tare da umarnin shiga shirin gyara hali, kasancewar ya riga ya shafe kusan shekaru uku a tsare.
Haka nan, Abdullahi Ali ya samu hukuncin shekaru 20 bayan ya amsa laifin samar da man fetur ga ’yan ISWAP. Duk da rokon sassauci da ya yi, kotun ta tabbatar da hukuncin.
Auwal Bello shi ma an yanke masa hukuncin shekaru 10 kan laifin daukar nauyin ta’addanci, ciki har da biyan haraji ga kungiyar da kuma saukaka mu’amaloli da suka kai sama da Naira dubu dari bakwai da hamsin a lokacin sauyin kudin Naira ga kungiyar.
Baya ga hukuncin zaman kurkuku, kotun ta kuma umarci wasu daga cikin wadanda aka yanke wa hukunci da shiga shirin gyara hali da kawar da ra’ayin ta’addanci.
A halin yanzu, kotuna kusan goma na gudanar da shari’o’in ta’addanci sama da dari a lokaci guda, abin da hukumomi ke cewa na nuna kokarin daidaita martanin Najeriya kan ta’addanci da kuma tabbatar da adalci ga wadanda suka gamu da hare-haren ’yan ta’adda.