Kotu ta yanke wa matasa biyu hukuncin ratayewa
Babbar Kotun Jihar Kano ta 13 ta yanke wa wadansu matasa biyu hukuncin kisa ta hanyar ratayewa bayan samunsu da laifin kisan kai. Takardar kara da aka gabatar a kotun ta bayyana cewa a ranar 7 ga Disamban 2001, Haruna Balarabe Tudun Wazirci ya kashe wani Abubakar Idris Sagagi ta hanyar daba masa adda a […]
Babbar Kotun Jihar Kano ta 13 ta yanke wa wadansu matasa biyu hukuncin kisa ta hanyar ratayewa bayan samunsu da laifin kisan kai. Takardar kara da aka gabatar a kotun ta bayyana cewa a ranar 7 ga Disamban 2001, Haruna Balarabe Tudun Wazirci ya kashe wani Abubakar Idris Sagagi ta hanyar daba masa adda a kai.
Shi kuma Bala Muhammad da ke zaune a Karamar Hukumar Nasarawa an same shi da laifin kisan Abdullahi Yakubu a ranar 4 ga Fabrairun 2014 lokacin da yake dawowa daga masallacin Juma’a.
A zaman kotun, Lauyan Gwamnati Barista Muhammad Balarabe ya gabtar wa kotun shaidu hudu, kuma wadanda ake zargin sun gaza kare kansu kan laifuffukan. Da yake yanke hukunci, Alkalin Kotun Mai shari’a Ibrahim Musa Karaye ya ce kotu ta gamsu da shaidun masu kara ta kuma yi watsi da shaidu kariya don haka ta yanke wa matasan hukuncin kisa ta hanyar ratayewa a karkashin sashe na 221 na Kundin Final Kod.