Kotu ta yanke wa matashi ɗaurin wata 6 kan satar kaza
“Bayan ya amsa laifinsa a gaban Alƙali O.F. Adeduntan, an same shi da laifin kuma kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari.”

Wata kotun majistare da ke zamanta a Ago Iwoye, Jihar Ogun, ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 21, Adebanjo Segun, hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari bisa samunsa da laifin satar kaza.
Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar tsaro ta Civil Defence , Dyke Ogbonnaya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
An ce an fara samun matsalar ne a ranar Laraba, 19 ga Fabrairu, 2025, kan Adebanjo mai shekara 21 a lokacin da aka kama shi da laifin satar kaza.
- Zulum ya rage adadin tallafin rabon abinci da kashi 90 a Borno
- An shiga ruɗani bayan Obasa ya koma majalisar Legas da ’yan sanda
Ogbonnaya ya bayyana cewa, “Bayan an yi nazari sosai kan lamarin tare da kammala bincike, an gano cewa wanda ake tuhuma ya aikata irin wannan laifin a wani lokaci a watan Disambar 2024 inda aka yi masa afuwa a matsayin wanda ake zato da ya yi laifin farko.
“Saboda bayyana laifin da ya aikata a baya, an gurfanar da shi a gaban Kotun Majistare ta Ago-Iwoye kan tuhume-tuhumen da ya shafi sashe na 430 na dokokin manyan laifuka na Jihar Ogun, Nijeriya 2006, a ranar 20 ga Fabrairu, 2025.
“Bayan ya amsa laifinsa a gaban Alƙali O.F. Adeduntan, an same shi da laifin kuma kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari.”
Hakazalika, an kuma yanke wa wani Kazeem Tobi mai shekara 20 hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari bisa samunsa da laifin satar janareta na Elepaƙ wanda kuɗinsa ya kai kusan N120,000 kacal.
An ce an sake gurfanar da Tobi a ranar Talata, 4 ga watan Fabrairu, 2025, kuma bayan da aka yi nazari sosai a kan lamarin, an gurfanar da shi a gaban Kotun Majistare ta Ago-Iwoye kan tuhume-tuhume biyu da suka shafi haɗa baki wajen aikata laifi da kuma mallakar wani abu da ake zargin an sace.