Kotu ta  yanke wa matashi hukuncin ratayewa

Babbar Kotun Jihar Kano da ke Titin Miller a Kano, ta zartar wa wani matashi mai suna Abubakar Idris Danhabu hukuncin kisa ta hanyar ratayewa sakamakon samunsa da laifin kisan wani matashi mai suna Shazali Mahmud, mazaunin Layin Gidan Kara a Unguwar Kurna, Kano. A ranar 30 ga watan Disamban 2012 ne, matashin ya hada […]

Kotu ta  yanke wa matashi hukuncin ratayewa
Kotu ta  yanke wa matashi hukuncin ratayewa

Babbar Kotun Jihar Kano da ke Titin Miller a Kano, ta zartar wa wani matashi mai suna Abubakar Idris Danhabu hukuncin kisa ta hanyar ratayewa sakamakon samunsa da laifin kisan wani matashi mai suna Shazali Mahmud, mazaunin Layin Gidan Kara a Unguwar Kurna, Kano.

A ranar 30 ga watan Disamban 2012 ne, matashin ya hada baki da wani mai suna Abba Lado wanda ya gudu, inda ya daba wa marigayin wuka a kirji, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take.

Hakan ya janyo aka tuhumi matashin da laifuffukan hadin baki da kisan kai, laifuffukan da suka saba wa sashe na 97 da sashe na 221 na Kundin Shari’a na Final Kod.

Lauyan masu kara, Barista Mahmood Balarabe ya gabatar da shaidu guda biyar yayin da lauyan kariya, Barista Kamaludeen Yahaya ya gaza gabatar da shaida ko guda daya.

Alkalin Kotun Mai shari’a Ibrahim Musa Karaye ya bayyana cewa ya yanke hukuncin ne bisa lura da yanayin yadda wanda ake kara ya yi amfani da wuka a wurin da ya tabbatar zai iya hallaka mutum. Haka kuma ya bayyana cewa an yanke hukuncin ne don ya zama darasi ga na baya.