Kotu ta yanke wa mutum 2 hukuncin kisa kan kashe ango a Kano

Kotun ta zartar musu da hukuncin bayan tabbatar da laifin da suka aikata.

Kotu ta yanke wa mutum 2 hukuncin kisa kan kashe ango a Kano

Wata Babbar Kotu a Jihar Kano, ta yanke wa wasu maza biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya, sakamakon samun su da laifin kashe wani sabon ango lokacin da suka yi masa fashi.

Mutanen sun haɗa da Aliyu Hussaini da Amir Zakariyya, an same su da laifin haɗa baki, fashi da makami da kuma kisan Yazid Haruna.

Alkalin kotun, Amina Adamu-Aliyu, ta ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin ba tare da wata shakka ba, tare da bayyana kisan a matsayin abu mai tayar da hankali.

Lauyan gwamnati, Lamido Abba Sorondinki, ya shaida wa kotu cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:47 na daren ranar 11 ga watan Yuni, 2025, a unguwar Sheka Sabuwar Abuja da ke Ƙaramar hukumar Kumbotso a Jihar Kano.

Ya ce waɗanda ake tuhuma sun kai wa mamacin hari da wuƙaƙe da adda, inda suka ƙwace masa wayoyi biyu da kuma kuɗi Naira 19,500.

Sun soki Haruna da wuƙa a wurare daban-daban, kuma daga bisani ya rasu sakamakon raunukan da ya samu.

Ko da yake waɗanda ake tuhuma sun musanta zargin tare da roƙon kotu ta tausaya musu.

Kotun ta same su da laifi ƙarƙashin kundin dokar Penal Code na Jihar Kano.

Kotun ta yanke musu hukuncin ɗaurin shekara ɗaya kan haɗa baki, ɗaurin rai da rai kan fashi da makami, da kuma hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin kisan kai.

Tun da farko, a watan Oktoban 2025, an riga an yanke musu hukuncin kisa saboda kashe wani malamin jami’a da suka yi a wani fashi da suka yi.

An gano baƙin haure 30 a ɓoye cikin tankar mai a Turkiyya

An tsare ɗan gwagwarmaya kan sukar gwamnatin sojin Nijar

Alhazan Kebbi rukunin farko sun dawo gida

Rukunin farko na Alhazan Kebbi 426 sun dawo gida