Kotu ta yanke wa mutum biyar hukuncin kisa kan mutuwar Khashoggi
Wata kotu a Saudiyya ta yanke wa mutum biyar hukuncin kisa bayan tabbatar da samun su da laifin kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi. Shi dai Khashoggi, wanda aka kashe a bara, ya shahara ne wajen caccakar gwamnatin Saudiyya kuma wasu jam’ian gwamnatin Saudiyyar ne suka kashe shi a offishin jakadancin kasar da ke birnin […]
Wata kotu a Saudiyya ta yanke wa mutum biyar hukuncin kisa bayan tabbatar da samun su da laifin kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi.
Shi dai Khashoggi, wanda aka kashe a bara, ya shahara ne wajen caccakar gwamnatin Saudiyya kuma wasu jam’ian gwamnatin Saudiyyar ne suka kashe shi a offishin jakadancin kasar da ke birnin Santambul na Turkiyya.