Kotu ta yanke wa Robinho hukuncin zaman waƙafi na shekara tara kan laifin fyaɗe

Kotun Italiya ta ce dan wasan zai zaman waƙafin ne a Brazil ba sai an miƙa mata shi ba.

Kotu ta yanke wa Robinho hukuncin zaman waƙafi na shekara tara kan laifin fyaɗe

Robinho, Brazil

Wata Kotun Italiya ta yanke wa tsohon dan kwallon Manchester City da Real Madrid, Robinho hukuncin zaman gidan yari na shekara tara bayan samunsa da laifin fyaɗe.

An samu Robinho mai shekara 40 da laifi a wata kotu a Italiya a 2017, wanda yana cikin taron dangin fyaɗe da aka yi wa wata matashiya ’yar Albania mai shekara 22.

A yanzu haka Robinho yana zaune a Brazil, wanda ba a miƙa shi Italiya ba, to amma alƙalai a Brazil sun yanke hukunci ranar Laraba cewar zai yi zaman yari a kasar kamar yadda Italiya ta buƙata.

Lauyoyi sun ce yana da lokacin da zai ɗaukaka kara kafin hukuncin ya fara aiki a kansa, wanda tuni tsohon tauraron kwallon ƙafar ya aiwatar.

Tsohon dan wasan tawagar Brazil da ya buga wa kasar wasa 100, yana taka leda a AC Milan a lokacin da aka aikata laifin da aka zarge shi.

A shekarar 2020 aka samu dan wasan da laifin aikata fyaɗe n, bayan da ya yi rashin nasarar ɗaukaka kara, inda wata kotu a Italiya ta tabbatar masa da hukuncin.

Daga nan ne masu shigar da kara a Italiya suka miƙa takardun izinin kamo shi daga Brazil.

Robinho wanda ya yi kaka biyu a Manchester City, ya sanar da wani kamfanin dillacin labarai a Brazil cewar da amincewar matar aka yi lalata da ita.

Robinho ya ɗauki kofin La Liga biyu a kaka hudun da ya yi a Real Madrid daga nan ya koma Etihad a matakin wanda aka saya mafi tsada a Birtaniya kan £32.5m.

An kuma sayi dan kwallon a ranar karshe da za a rufe kasuwar cinikin ’yan kwallo a Satumbar 2008 — kuma a karon farko da Sheikh Mansour ya fara aiki a matakin wanda ya mallaki Manchester City.

Bayan kaka biyu da City daga nan Robinho ya koma AC Milan, kungiyar da ya yi kaka biyar daga nan ya koma China a kungiyar Guangzhou Evergrande.

Bayan da ya kammala taka leda a China, sai ya koma Brazil a ƙungiyar Atletico Mineiro.